An gurfanar da Emefiele kan zargin mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya

Daga BASHIR ISAH

An gurfanar da dakataccen Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, a Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Legas bisa zargin laifuka biyu da suka haɗa da mallakar bindiga da alburusai ba bisa ƙa’ida ba.

Majiyarmu ta ce jami’an DSS ne suka shigo da Emefiele ɗin kotun da safiyar ranar Talata.

Zaman kotun ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nicholas Oweibo.

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Joseph Daudu, shi ne ya jagoranci tawagar lauyoyin da ke kare Emefiele ɗin.

Kodayake dai Emefiele ya musanta tuhumar da ake yi masa, inda ya ce bai aikata wani laifi ba.

Bayan sauraren ƙarar da aka karanto lauya Daudu (SAN), ya faɗa wa kotun cewa makonni biyu ana tsare da wanda yake karewa.

Kazalika, ya shaida wa Alƙali Oweibo an shigar da neman belin wanda yake karewa kuma mai ƙara ya san da haka.

A ranar 9 ga Yuni Shugaban Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele, sannan kwana guda bayan haka DSS suka ce sun yi ram da shi.