Zubar da jini laifi ne, kuma Allah yana fushi da wanda ya zubar da jinin, wannan ga waɗanda suka yarda cewa akwai Ubangiji. Da wane laifi za ka kashe mutum bayan da cewa bai kamata a zubar da jinin ɗan Adam ba? Duk da cewa akan iya samu wasu basu yarda da akwai Allah ba, amman bana tunanin akwai wanda bai yarda da ɗan adamtaka ba.
Mu a gari na alfarma (Gwoza), wanda mune na biyu a yawan jama’a a jihar Borno, tare da mutane masu daraja. Allah ya azurta mu da iyaye masu iliimi, da kuma ’ya’ya masu hazaka. Ga yawa, ga basira, ga ilimi, amman abubuwa sun fi ƙarfin mu. Yawan mu, da ilahiran abubuwa da muka mallaka duk sun tafi a tutar babu.
Tun 2011, muna fama da rikicin Boko Haram, ina tunanin ya kamata ace an kai ga lokacin da za aji ce wa babu komai yanzu, sai dai saɓanin haka muke fuskanta.
Abin nan, ya fara da ɗauki dai-dai, yakai ga karɓan garin gaba ɗaya. Sun kashe mana baban mu abin alfaharin mai Sarki mai daraja Shehu Mustapha Idrisa Timta, sannan garin ya rincaɓe baki daya. Basu bar mu iya nan ba, gaba ɗaya an maida mutanen mu rogaye, mutane ba zasu iya fita noma ba, sai dai a basu. Idan ma sun fita za a kashe su.
Muna fuskantar barazana, da yau ko gobe ɗayan mu zai iya zama babu shi. Saboda bamu san waye ne abun zai faru da shi gobe ba.
A hakan, ba su kyale mu ba, zai gashi wannan shekarar ma kamar bara sun zo mana da sabon salo na ƙunar baƙin wake. Hakan yasa mutanene da yawa suka rasa rayukan su, wasu kuma sun tafi kenan koda kuwa a ce suna raye.
Me yasa nace haka? Wani har abadan ya rasa hannun sa, wani zai rasa ƙafafuwan sa, yayin da wasu sun rasa wani sassa na jikin su. Kamar yadda ya faru a shekara ta 2014, akwai wanda har yau ya rasa haihuwa, duk saboda rikicin Boko Haram dinan.
Waɗannan kashe-kashen, da kuma hare hare da yake faruwa. Na kasa gane wa, mugunta ne, ko jihadi, ko kuma wasu ne ke anfana da shi. Idan wasu ne ke anfana da shi to su waye? Idan kuma ba a sani ba me yasa aka kasa sani? Laifin su waye ne? Shuwagabannin mu? Su waye su? Me aikin su? Me ya kamata su yi mana?
Gaskia in tabi takan layin kowa a faɗe ta. Idan har shuwagabannin mu sunyi magana a sama kuma ba a ji musu ba to kenan wane mataki suka ɗauka? Idan anki a saurare su ne, su fito suyiwa al’umma bayani. To, ba wannan ba, idan akayi haka za a ce mun saɓawa shugabanni, haka ne, ba ina nufin ɓata sunan wani ba. Babu wanda zamu ɓata sunan shi sai dai wanda ya yaɓawa fuskar sa baƙin penti. Bama nufin kowa da sharri, abinda muke bukata anan zaman lafiya da cigaba. Idan ka ɓata sunan wani ba karuwa zaka yi da komai ba haka zalika kuma, yin shiru ba tare da ankarar da su ba, wani abu ne daman, da munin sa ya fi yin magana din.
Har ila yau, iyaye na kuyi haƙuri, akwai laifin ku a ciki. Ba zaku iya magana ba, kuma kun ce kar muyi magana. An dake mu, sannan kunce kar muyi kuka, ya kuke ganin zamu kalle ku daku da waɗanda suke dukan mu? Ƙaddara ma misali ace baku da alaƙa da masu kashe mu, tayaya hankalin mai tunani zai yarda? Kunyi shiru kunki kuyi magana kuma kunce kar muyi magana, to mesa? Ko don saboda ba a kashe ‘ya’yan ku bane? Kodan abin bai shafe ku bane? Kamar yadda muka ɗauke ku iyayen mu dolen ku kuma ku ɗauke mu a matsayin ‘ya’yan ku. Dan haka, abinda ya shafe mu ya shafe ku, abinda ya shafe ku ma ya shafe mu.
Ku fito, ku nuna ɓacin rai a majalisa, babu adawa, fashe kariya kawai muke nema.
Ba zanyi dogon surutu ba, face mu dai muna fatan Allah ya kawo mana sauƙi, Allah kare mana ku, ku bi mana haƙƙin mu, idan kuma ba zaku iya ba, mu haɗu a rubutu na gaba..!
Daga MUHAMMAD ALBARNO, +2348034400338.