Daga AISHA ASAS
Shugaban hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-mustapha ya kafa wani kwamiti na musamman da za su yi aikin tsaftace masana’antar finafinai ta Kannywood.
A wata sanarwar wadda ta fito ta hannun Abdullahi Sani Sulaiman Jami’in Watsa Labarai na Hukumar Tace Finafinai, ta bayyana cewa, an kafa kwamitin ne don ganin an cimma ƙudurin sabunta rijista ga kowane ɗan masana’antar, matakin da ta ɗauka da muhimmanci.
El-mustapha ya ce, manufar kafa kwamitin shi ne shiga lungu da saƙo na masana’antar domin tabbatar da kowa ya mallaki rijistar da ke nuna shaidar mutum cikakken ɗan masana’anta ne tare da tabbatar da masu shiryawa tare da ɗaukar nauyin fınafinai sun bi dokar karɓar shaidar ɗaukar finafinai daga hannun hukumar, wato ‘shooting permit’.
Da yake bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin wakilan kwamitin, Abba El-mustapha ya ce, hukumar ta yi la’akari da ɓangarorin masana’antar daban-daban inda ta zaɓo mutane kamar haka:
1 Tijjani Abdullahi Asasi (Actors Guild) Shugaba.
2 Ali Muhd (KSCB) Mamba
3 Aina’u Ade (Actors Guild) Mamba
4 Aminu Muhd Sabo (Actors Guild) Mamba
5 Jazuli labaran Gwale (KSCB) Mamba
6 Abubakar Usaini Alaramma (Arewa Films Markers) Mamba
7 Ismail Khalil Jaen (MOPPAN) Sakatare.
Da yake jawabin karɓar aikin da aka ba su amadadin ‘yan kwamitin, Malam Tijjani Abdullahi Asasi ya gode wa Shugaban Hukumar Tace Finafinai, Abba El-mustapha, bisa la’akari da cancantar su na zaɓo su domin yin aikin, inda ya yi roƙo ga hukumar da ta ba su cikakken haɗin kai da goyan baya ta yadda zasu gudanar da aiyyukansu cikin nasara.
Daga ƙarshe ya sha alwashin gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa tare da tsaro ba kuma da nuna bambancin siyasa.
