Laifi ne sakin fim ko bidiyon kiɗa ba tare da shedar hukumar NFVCB ba – Gwamnatin Tarayya 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A cewar Gwamnatin Tarayya, sakin waƙoƙi, ko finafinai, ko kuma bidiyon kiɗa ba tare da Hukumar Kula da Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta bayyanar da gurbinsa ba zai iya zama wani nau’in cin zarafi.

Rarraba finafinai ta hanyar saka shekarun da ya kamata akai kafin a kalla kan taimaka wurin tantance finafinan da suka dace da waɗanda ba su dace ba ga kallo.

Baya ga haka, hanya ce da ke sawaƙa wa iyaye zaɓawa ‘ya’yansu finafinai da suka dace da su, da kuma sanin waɗanda bai kamace su kalla tare da yaransu ba.

A watan Mayu, hukumar ta sanar da shirye-shiryen fara rarraba abubuwan sauraro na sauti, kamar skits da bidiyon kiɗa.

Shaibu Husseini, babban daraktan hukumar, ya bayyana cewa, akwai buƙatar a ƙara ƙaimi wajen tantance bidiyoyin da ake kallo a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa, babban daraktan ya ce, NFVCB ta fara shirye-shirye ƙirƙirar ” babbar cibiyar rarraba finafinai da bidiyo.”

Ya kuma gargaɗi masu ƙirƙira da su guji fitar da skits, finafinai, ko bidiyon kiɗa ba tare da rarrabawa daga hukumar ba.

Shugaban NFVCB ya ƙara da cewa, hukumar ta haɗa kai da jami’an tsaro domin bin diddigin ‘yan fim da aka samu da laifi.

“Haka zalika laifi ne a raba ko nuna duk wani fim ko bidiyo da ya haɗa da skit da bidiyon kiɗe-kiɗe a kowane kafa ta sadarwa ba tare da neman Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa don tantancewa ba,” inji shi.

Ya kuma ƙara da cewa, “Saboda haka hukumar na sanar da cewa, muna aiki tare da jami’an tsaron da abin ya shafa domin bin diddigin mutane da kamfanonin da ke fatali da wannan umurnin, kuma za mu yi duk mai yiwa don ganin sun fuskanci fushin doka.

A ɓangare ɗaya, hukumar ta NFVCB ta nuna takaicinta kan yawaitar tallatawa da yaɗa finafinan batsa a kafafen sada zumunta. 

“Ina so in tunatar da masu shirya finafinai da masu yin ƙananan bidiyo cewa, laifi ne a Nijeriya nunawa kai tsaye ko a kaikaice a taruka na daga ababen da suka dangci jima’i,” inji shi.

NFVCB na bayar da takardar shedar tantancewa akan duk wani fim da ayyukan bidiyo da kwamitin cikin gida ke tantancewa. Inda akan rattaba ɓangaren da fim ɗin ko bidiyon ya faɗa, wato bayyana shekaru da ya kamata akai kafin a kalli fim ɗin sakamakon tsaurin kalaman da ke ciki ko ababen da ake nunawa na yawaitar batsa ko ta’addanci da sauransu.

Hukumar tana amfani da wasu alamomin da za su iya ganar da mai shirin siyan fim ko kallon waƙar idan ta dace da ya kalla. Wasu daga cikin alamomin akwai;”G” don nuni na gabaɗaya, wato kowa ma zai iya kalla. Sai kuma “PG” wanda ke nufin yara za su iya kalla, amma tare da jagorancin iyaye, don yana ɗauke da ababen da ka iya ɗaure masu kai, su kuma iyayen sai su masu bayani don gujewa mummunar fassara. 

Akwai kuma”C” wanda ke nuni da finafinai da aka yi su musamman don yara.

Akwai kuma alama ta “12” wanda ke nuna bai kamata yaro ɗan ƙasa da shekaru 12 ya kalla ba. Sai kuma “12A” da ke bayyana cewa, babu ɗan ƙasa da shekaru 12 da zai iya shiga sinima har sai dai idan ya kasance tare da babba.

Kuma daga cikin alamomin da hukumar ta NFVCB ke amfani da su akwai, “15” don nuna cewa, ba a ba da shawarar kallon fim ɗin ga mutanen da ke ƙasa da shekaru 15 ba, yayin da alamar “18” ke nuna cewa don manya ‘yan sha takwas zuwa sama kawai aka yi shi. 

By ukarofi