Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 1.5 ga furodusoshi don gudanar da ayyukan fim

Daga AISHA ASAS 

A ƙarkashin tsarin ‘Renewed Hope Agenda’ na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta raba wa masu shirya finafinai Naira biliyan ɗaya da rabi domin gudanar da ayyukansu.

Wannan shiri wani ɓangare ne na Asusun Ƙirkira, mai kimanin Naira Biliyan 5, da aka ƙaddamar tare da haɗin gwiwa da Bankin Proɓidus a watan Disamba 2023.

Tun daga farko dai an fara bayar da kuɗaɗen ne a watan Mayun shekarar 2024, kuma an ware Naira biliyan 1.5 ga ’yan wasa huɗu da furodusoshi.

Fegho Umunubo, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa akan ƙirkirar zamani da ke ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“Bayan an samu nasarar raba Naira biliyan 1.5 ga ‘yan wasa huɗu da furodusoshi don gudanar da ayyukansu na finafinai, muna sanar da cewa har yanzu a shirye muke don bayar da tallafin wasu ayyukan ƙirkira. Don haka, idan kun san wani da ke neman kuɗi don gudanar da ayyukansu na ƙirƙira, to ku isar da wannan adireshin imel zuwa gare su: Creatiɓes@proɓidusbank.com,” inji Fegho.

A halin yanzu dai an fara aikin tantance kaso na biyu na masu neman tallafi daga asusun na Naira biliyan 5. 

Masana’antar ƙirkira ɗaya ce daga cikin ɓangarorin ƙasar da ke saurin bunƙasa, kuma wannan tallafin na nufin samun gagarumin cigaba a ɓangaren. 

Baya ga asusun na ƙirkire-ƙirƙire, Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwa da Bankin Raya Afirka, wato AfDB, na shirin fitar da wani asusun IDICE na dala miliyan 617 don ciyar da fasahar zamani da masana’antar ƙere-ƙare gaba.

Shirin iDICE, shiri ne na tsayin shekaru biyar, wanda aka ƙaddamar don yin amfani da fasahohin zamani a matsayin wata hanya ta ci gaban arzikin ƙasa da kuma sanya Nijeriya a jerin ƙasashen da ke cin moriyar fasahohin zamani ta fuskar cigaban tattalin arziki.

Wannan shirin na dalar Amurka miliyan 617.7, Bankin Raya Musulunci (IsDB), Bankin Masana’antu (BOI), da AfDB ne suka ɗauki nauyin shi.

Bugu da ƙari, a shekarar 2023 gwamnati ta ba da tallafi ga ’yan kasuwa masu cin gashin kansu, inda ta samar da Naira miliyan 2-5 a kowacce sana’a don fara kasuwanci a jihohin Enugu da Jigawa.

Wannan yunƙurin, wanda aka fara bayar da shi a watan Mayu 2024, ya tallafa wa waɗanda suka kammala samun horon sana’ar kayan sawa, wanda ya ba su damar amfani da ilimin wurin haɓaka kasuwancinsu daga kuɗaɗen da suka samu.

Har ila yau, gwamnatin ta samar da dala miliyan uku na ƙasa da ƙasa don horar da masana’antar ƙere-ƙare tare da haɗin gwiwa da kamfanonin Faransa.

Wanda haɗin gwiwar ke nufin haɓaka ƙwarewar masu ƙirƙira na Najeriya, da ba su damar yin gogayya da ƙasashen duniya.

Haka kuma, bikin baje koli na NaijabrandChick, an samar da jarin Naira miliyan ɗaya ga kowane kasuwanci, daga cikin kasuwanci guda uku masu nuna al’adu da ƙere-ƙare a ɓangaren fasahar zamani. Wannan yunƙurin, wanda ya fara a watan Mayu 2024, yana ba da babban jari ga sabbin masana’antu na waɗannan ɓangarorin. 

Kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana, ɓangaren ƙirkire-ƙirƙire na Najeriya, na ƙunshe da sassa biyar: Midiya da ɓangaren nishaɗantarwa, Ƙyale-ƙyale da tsarin rayuwa, zane-zane, da yawon buɗe ido da karɓar baƙi.

A halin yanzu dai, ɓangaren na ɗaukar mutane kusan miliyan huɗu da ɗari biyu ma’aikata a cikin waɗannan ƙananan sassan. Hasashen ya nuna cewa, sashen na ƙirkire-ƙirƙire kan iya samar da ƙarin ayyukan yi har miliyan 2.7 a cikin shekaru huɗu zuwa biyar masu zuwa.