A jiya ne muka samu rahoton garkuwa da wakilan Jaridar Blueprint da The Nation tare da iyalansu a gidajen su dake Danhono cikin garin kaduna.
Ƙungiyar yan Jaridu ta ƙasa ita ta fitar da wannan sanarwa da sa hannun shugaban ta. Sun bayyana wannan hari a matsayin rashin imani tsantsa. Abdulraheem Aodu shine wakilin Jaridar Blueprint, yayin da Abdulgaffar Alabelewe shine wakilin The Nation.
Sai dai masu garkuwar sun sako matar wakilin Blueprint saboda ba ta da lafiya sosai.
Ƙungiyar ƴan jaridun reshen kaduna sun yi kira da gwamnati da jami’an tsaro da su hanzarta wanjen ganin an kuɓutar da yan jaridun tare da iyalansu.
