
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shekaru ashirin da suka gabata da rasa mahaifinta a hatsarin jirgin sojojin sama, Flight Lieutenant Damilola Adekunle ta sake haɗuwa da wata jarrabawa a wannan karon na rasa mijinta, wanda aka ɗaura musu aure ƙasa da makonni uku da suka gabata a makamancin hatsarin.
Mahaifin Adekunle, wato Wing Commander E.O. Adekunle yana ɗaya daga cikin jami’an rundunar Sojojin Sama na Nijeriya (NAF) da wani hatsarin jirgi ya rutsa da su a Jihar Benuwai a ranar 17 ga Satumbar 2006. Al’amarin ya auku ne a yankin Oko da ke Ƙaramar Hukumar Vandeikya a lokacin da jirgin na Dornier 228 ke ɗauke da manyan jami’an sojoji zuwa Jihar Kuros-Riba, kamar yadda Blueprint ta ruwaito.
Wannan hatsari ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an sojoji da dama da jefa iyalai cikin jimamin rashin makusantansu da aka tura su aiki na musamman.
Saidai wannan bai kawo ƙarshen jimamin irin al’amarin ba acikin iyalan Adekunle, domin yayin da Damilola take girma ɗauke da raɗaɗin tarihin rashin mahaifin nata, ƙaddara da sanya za ta sake cin karo da irin abin alhinin. A wannan karo, ta rasa mijinta da aka ɗaura musu aure a kwanan nan. Kwana 16 kaɗai auren nasu ya yi, domin a ranar 19 ga Satumba, 2026 ne aka ɗaura wa Damilola aure da Squadron Leader Ahamefule Aham Man-Ugwueje a Abuja, inda suka shirya shiga sabuwar rayuwa.
Wannan aure ya zo ƙarshe a 5 ga Oktoba, 2026 a lokacin da wani mummunan hatsarin jirgin sojoji na NAF 931, ATR-43 aircraft ya yi ajalin mutum 25 a yankin Igbokoda da ke Jihar Ondo, ciki har da mijina nata. Manhaja ta ruwaito cewa, hatsarin na kwanan nan ya auku ne a lokacin da jirgin sojojin ya nufi zuwa Legas daga Benin a wani yanayi na atisayen jami’ai a ranar Litinin.
Bayan atisayen bincike da ceto, hukumomi sun tabbatar da rasuwar baki ɗaya mutanen da ke cikin jirgin. Sannan, akan haka ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana makokin kwana uku domin karrama jami’an da iftila’in ya rutsa da su tare da miƙa ta’aziyyarsa ga makusantan mamatan kamar yadda shi ma Shugaban NAF, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya yi a wata sanarwa.
