Hisbah ta kama masu ƙwacen waya a masallaci a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Hizba a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, ta kama wasu matasa takwas da ake zargi da ƙwacen waya a masalallacin al-Fur’an da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa da ke jihar.

Kwamandan Hizba Sheikh Harun Ibn Sina, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.

Ya ce an kama waɗanda ake zargin da ranar Allah suna shan muggan ƙwayoyi da sauran ababen maye a kusa da masallacin.

Ibn Sina ya bayyana ɗabi’ar matasan da haramtacciya da ba ta dace ba a wannan wata mai alfarma na Azumin Ramadan.

Ya yi kira ga jama’a su ƙara sanya ido da kai rahoton duk wani abu da suka ga ya na faruwa da bai gamsar da su ba, ko wani mutum, su kuma hukumarsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki da hukunta wanda aka samu da laifi.