Mace na neman takarar wakiltar Gusau da Tsafe a Majalisar Tarayya

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD

Wata mata kuma ‘yar gidan sarauta, Hajiya Fatima Muazu Mayana, ta firto neman a zaɓe ta a zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC, don ta wakilci Mazaɓar Gusau da Tsafe a Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke Abuja.

A cewar ‘yar siyasar, “Ni haifaffiyar Gusau ce, ɗiyar Alhaji  Muazu Mayana. An haife ni ranar 3 ga Maris, 1982. Mu na da yawa, kuma gidanmu gidan sarauta ne mai dogon tarihi da ya kai shekaru 300.

“Na yi karatun islamiya, na halarci Makarantar Ibrahim Gusau, na zarce zuwa Makarantar Sakandare ta Nana da ke Sokoto, sannan na yi karatun digiri a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.”

Ta ƙara da cewa, duk da ta tashi da gata da kwarjini har a jami’a, amma hakan bai sa ta raina jama’a ba.

Fatima Mayana ta ce, ta kuma kafa Gidauniyar Binta Mayana ne, domin tallafa wa jama’a ta hanyar kiwon lafiya, ilimi da koya musu da sana’o’i. 

’Yar siyasar, wacce kuma ita ce Gimbayar Mayana, ta ce idan har aka zave ta a zaɓen fidda gwani da kuma na gama-gari, lallai za ta yi hoɓɓasa, don ƙarfafa wa marasa galihu da dukkan al’umma gwiwa.

Dangane da mamayar da maza suka yi wa harkar siyasa a jihar, ta bayyana cewa, “ni dai Ina neman goyon bayan a bar ni na wakilci jama’a, don a samar da romo da ribar dimokraɗiyya.”