Aisha Buhari ta roƙi ’yan takarar Shugaban Ƙasa na APC su zaɓi mace a matsayin mataimakiya

Daga AMINA YUSUF ALI

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai mai ɗakin Shugaban Ƙasar Nijeriya A’isha Buhari ta yi wani taron ganawa da masu zawarcin kujerar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023. 

A yayin taron ne A’isha ta isar da roƙon ta ga ‘yan takarar shugabancin ƙasar nan gabaɗaya da su zaɓi mata a matsayin abokan takarar tasu. ‘Ya takarar Su ne, Bola Ahmad Tinubu, sai mataimakin shugaban ƙasa mai ci a yanzu, Farfesa Yemi Osinbajo, sai Dakta Chris Ngige da sauransu. 

Chris Ngige ya yi kira ga takwarorinsa ‘yan takara da su yi biyayya ga abinda A’isha Buhari ta faɗa, wato su zaɓi mata a matsayin abokan takarar su  sannan kuma a yi siyasa ba da gaba ba. 

Mai ɗakin shugaban ƙasa wacce ta shirya taron bude bakin azumi ga waɗannan ‘yan takara ta ƙara da cewa, kamata ya yi duk wanda a cikinsu ya ci zaɓe ya tabbatar da ya ware wani kaso na musamman na muƙaman gwamnati ga mata domin a dama da su su ma. A cewar ta idan aka duba ƙoƙarin yadda mata suke dagewa wajen fitowa zaɓe ya cancanta a ba su damar a tafi da su a takarar mataimakiyar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa. A cewarta ymlokaci ya yi ma da kowanne ɗan takara a nasa matakin ya ɗauki mace a matsayin mataimakiyarsa a takarar muƙaminsa.

Sannan kuma uwargidan Buharin ta nemi ‘yan takarar da su tabbatar da zave mai zuwa ya wakana cikin adalci da salama kamar yadda zaɓen maigidanta a 2015 ya wakana. A cewarta wannan ita ce kawai babbar kyautar da za su iya yi mata ita da iyalanta. 

Taron dai ya samu halartar ‘yan takarar shugabancin ƙasar nan na Jam’iyyar APC da dama kamar Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna, Bala Muhammad na Bauchi, Ministan ƙwadago, Chris Ngige, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da sauransu. 

Kodayake rahotanni sun bayyana Rashin halartar Farfesa Yemi Osinbajo amma an ce ya tura wakilci ta hannun tsohon Gwamnan Jihar Edo, Oserheimen Osunbor.