Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Shugaban Hukumar Hana Ta’ammali da Fatauci da Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA), Mohammed Buba Marwa, ya tabbatar da yin lambar shaida wa kadarorin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda, Abba Kyari a cikin garin Maiduguri, yana mai nuni da cewar, dukkan kadarorin da jami’in ɗan sandan ya tara ta hanyar haram za su kasance mallakar gwamnati.
Da yake yin tsokaci kan wasu gidaje guda shida da wani katafaren kasuwar zamani da ya ƙunshi shaguna masu yawa mallakin Kyari, shugaban hukuma ya bayyana cewar, ba tare da yin nuni ga wani ɗan Nijeriya ma’abucin aikata ire-iren wannan laifi ba, akwai doka ta Nijeriya wacce ta yi tanadin ƙwace dukkanin waɗansu kadarori da wani mahaluki ya tara ta hanyar aikata laifi ko laifuka.
Idan za a iya tunawa dai, hukumar yin hani da ta’ammali ko safara da miyagun ƙwayoyi ta ƙasa a farkon wannan shekara ne ta cafke Kyari yayin da yake ƙoƙarin bai wa jami’in ta tagomashin toshiyar baki kan wani ƙunshin fodar ibilis da jami’an hukumar suka kama.
Saboda haka, hukumar ta lambace waɗancan kadarori dake garin Maiduguri da zummar yin bincike akan su.
Katafaren ginin mai bene hawa biyu wanda ya ƙunshi kasuwar ta zamani da ake zargin Kyari ne ya mallaka, da aka yi wa laƙabi da ‘Assurance Plaza’ yana zaune ne akan titin zuwa barikin soji mai laƙabin Giwa, kuma yana da shaguna kimanin guda 100.
Gidaje guda shida kuma da aka lambace a garin na Maiduguri, waɗanda har ila yau ake zargin Kyari ya mallaka, suna cikin rukunin gidajen ma’aikatan gwamnati ne da aka yi wa laƙabi da Gidajen GRA, kuma hakan ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da aka cafke wani ƙasurgumin mai fatauci da miyagun ƙwayoyi, Ukatu, wanda ake zargi da fasaƙwaurin ƙwayoyin tiramadol na kuɗin da ya kai Naira biliyan uku da kuma ake danganta ta ga Kyari da tawagar sa ta IRT.
