An gudanar da taron sasancin jam’iyyu a Nijeriya don samun fahimta

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

A ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da taron sasanci ga wasu jam’iyyun siyasar Nijeriya don samun cikakkiyar madogara da za ta kawo cigaba a siyasar ƙasar.

Taron wanda Gidauniyar Action Aids ta ɗauki nauyin gudanarwa ya samu halartar wakilan jam’iyyun siyasa daban-daban daga faɗin ƙasar nan, don ba matasa da mata damar yin shugabanci don su ma su samu tunani mai kyau.

Wasu daga cikin jam’iyyun da suka halarci taron sun haɗa da jam’iyyar ADC da ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano Hon. Balarabe Rufa’i ya wakilta, sai jam’iyyar PRP Nasara da Hon. Namatazu ya wakilta duk daga matakin Jihar Kano.

Sauran jam’iyyun sun haɗa da jam’iyyar APC mai mulki yanzu da kuma jam’iyyar adawa ta PDP, haka kuma akwai jam’iyyar YDP da kuma jam’iyyar YPP da dai sauran su.

A cikin jawaban da suka gabata yayin taron akwai batun bai wa matasa da matasa dama don kawo canji da samar da sabuwar rayuwar da za a inganta harkokin zamani da amfani da tunani mai kyau da zai iya kawo sauye-sauye a cigaban ƙasar nan.

Kazalika an yi ƙorafi dangane da irin jam’iyyar APC ta sa kuɗin sayen fom na takara daga matakin shugaban ƙasa ya zuwa ɗan majalisar jiha da tsada da zai iya kawo tsaikon ga kudurin mata da matasa kan ba su damar tsayawar takarar su, inda sauran jam’iyyun suka nemi APC ta rage wannan kuɗi na fom da ta sa don sauƙaƙawa.

Taron dai an gudanar da shi ne a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, sannan ya kuma samu halartar manyan ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da kuma sauran masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen ƙasar nan.