Matasan Bade/Jakusko za su saya wa Hon. Kaitafi fom don yin takarar Majalisar Wakilai

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu 

Biyo bayan kiran da matasan ƙananan hukumomin Bade/Jakusko a Jihar Yobe su ka yi na kira ga hadimin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, wanda hakan ya jawo a makonnin da suka gabata hadimin ajiye muƙamin shi, kamar yadda doka ta tanada, tare da bayyana gamsuwarsa kan wannan buƙata ta al’ummar yankin.

Bugu da ƙari kuma, a wannan makon uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta shelanta fara sayar da fam ga yan takara a kowane mataki na neman tsaya wa takara, wanda ganin haka, matasan suka bayyana cewa sun ɗauke wa matashin ɗan siyasar; Hon. Kaitafi ɗawainiyar sayen fam ɗin tsayawarsa takara, tare da ɗawainiyar yaƙin neman zave da makamantan su, wanda nan take matasan suka ayyana buɗe asusun karo-karo a tsakanin su don tara kuɗin da za su masa fam ɗin takarar kujerar majalisar wakilai a zaɓen 2023 mai zuwa.

Wakilinmu ya gano cewa wannan mataki da matasan suka ɗauka shi ne irinsa na farko a tarihin siyasar yankin, sannan kuma hakan yana zama ‘yar manuniya dangane da farin jinin Hon.

Kaitafi a zukatan al’ummar yankin, haka kuma saƙo ne mai cike da armashi kan irin yadda matasan ke hanƙoron samun kyakkyawan wakilci a zauren majalisar wakilan wanda suka sha ƙorafi kan halin ko-in-kula da wasu masu riƙe da madahun iko ke nuna wa matasa tare da zarge-zargen rashin taɓuka abin a zo a gani da wasu ‘yan siyasa a yanki ke yi. 

Bugu da ƙari, wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban asusun tattara kuɗaɗen, Alhaji B. Muhammad Gashuwa, inda ya warware zare da abawa kan sha’anin tare da bayyana cewa, “Alhamdulillah, wannan haɗaka ce ta jam’iyyun siyasa daban-daban masu kishin ci gaban wannnan yanki, inda muka haɗu kuma mu ka buƙaci Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, domin ya wakilci waɗannan qananan hukumomi namu. Kuma kasancewar ya amsa wannan kira namu, bayan ya nemi izinin Gwamnan jihar Yobe da uban-gidan shi, shugaban majalisar Dattawan Nijeriya tare da sanya masa albarka shi ne muka ga ya dace mu da kanmu mu tara kuɗaɗen da za a kashe a takarar.”

“Shi ne muka shiga mu ka zauna don tsara yadda al’amarin zai gudana ta fannin yin rijista da hukumar ‘Cooperate Affairs’, hukumar kula da biyan haraji ta gwamnatin tarayya (FRIS) tare da duk ɓangarorin da abin ya shafa a ƙaramar hukumar Bade a jihar Yobe, wanda a ƙarshe muka buɗe wannan asusun ajiya na banki.

Wanda ta wannan tallafin da jama’a zasu saka a asusun za mu saya masa fam ɗin takara, kuma mu yi zirga-zurgar yakin neman zaɓe da sauran abubuwan da takarar ta ƙunsa; in sha Allah.” 

“Haka kuma, yanzu haka zancen da muke da kai, ƙasa da awanni 24 da buɗe wannan asusun mun samu sama da Naira miliyan biyu. Sannan ƙudirin da muke da shi kan haka shi ne a matsayin Alhaji Sani Kaitafi mai taimakon al’umma, koda mun samu sama da miliyan 100 ba zai zama damuwa ba ganin cewa waɗanda suka kafa wannan gidauniyar mutanen ne masu kwatanta adalci da sanin ya kamata, za mu yi amfani da sauran kuɗin da suka rage bayan kammala ɗawainiyar zaɓe; wajen raba su ga mabuƙata a cikin al’ummar mu.

Saboda ba ma son Hon. Ahmed Kaitafi ya saka sisin-kwabon sa a tsayawa takarar sa a Bade/Jakusko. Kuma hatta zuwa wajen sayen fam a ofishin uwar jam’iyyar APC mun ɗauke masa, mu ne za mu je mu saya sannan mu miƙa masa.”

A nashi ɓangaren kuma, Babban Sakataren asusun tattara kuɗaɗen, Nasiru Alhaji Auwal Mai-manja ya bayyana cewa, a matsayin su na matasa kuma masu kishin yankin, shi ne suka yanke shawarar samar da asusun; ba tare da masaniyar Hon.

Sani Ahmed Kaitafi ba. Sannan ya sanar da cewa, hakan ne ta dalilin nagartar da yake da ita tare da dimbin alhairan da ya shuka wa jama’ar wadannan ƙananan hukumomi na Bade da Jakusuko  al’amarin da babu wanda zai musanta hakan. 

“Kaɗan daga cikin abubuwan alhairan da ya aiwatar don inganta rayuwar al’ummar mu sun haɗa da bayar da tallafi a fannin ilimi, biya wa ɗalibai kuɗin karatu, sayen littafai, kayan karatu, kwamfotoci ga ɗalibai.

“Gina rijiyoyin burtsatse a wurare daban-daban, tallafin gina masallatan Jummu’a kimanin biyar, bai wa mata sama da 200 jari da yan kasuwa da sauran su. Sannan na san ya bayar da kyautar motoci ga jama’a sama da 15 cikin kasa ga watanni biyu. Sannan da tallafi a harkar noma da kiwon lafiya.”

By Editor