Jami’in sashen fasahar sadarwa na hukumar hisbah a Dandume, Abdul Baƙi Almustapha Dandume, ya fitar da sanarwar haka.
Sanarwar ta ce, jami’an Hisbah a ƙarƙashin jagorancin D.C Malam Bashir Lawal Balarabe sun gudanar da sintiri a unguwanni da kasuwannin Dandume, inda suka kama mutanen suna ikirarin bayar da maganin aljanu, mayu da neman kuɗi, bugun ƙasa, tare da amfani da hotunan batsa wajen yaudarar mutane.
A cewar bayanin, jami’an sun kama mutanen ne yayin da suke gudanar da irin waɗannan ayyuka a fili a cikin kasuwar Dandume, lamarin da hukumar ta bayyana a matsayin barazana ga tarbiyya da kyawawan ɗabi’un al’umma.
Hukumar Hisbah ta ce za ta cigaba da gudanar da sintiri a gari da kasuwanni domin kama duk masu aikata irin waɗannan laifuka, tare da jaddada cewa za a ɗauki matakan ladabtarwa da suka dace kan waɗanda aka kama bayan kammala bincike.
