Hoto: Yadda jana’izar Bantex ta gudana a Kaduna

A wannan Lahadin aka gudanar da jana’izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Architect Barnabas Yusuf Bala da aka fi sani da Bala Bantex.

Jana’izar ta samu halartar manyan baƙi na kusa da nesa, ‘yan siyasa, jami’an gwamnati da sauransu.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar, wanda bayan kammalawa ya nuna godiyarsa a madadin Gwamnatin Kaduna ga ɗaukacin waɗanda suka halarci jana’izar kamar dai yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *