Yau Buhari zai tafi London

Daga UMAR M. GOMBE

A wannan Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi Landon don halartar wani babban taro na duniya kan batun ilimi, wato Global Partnership for Education (GPE) na 2021 zuwa 2025.

Hadimin Buhari kan sha’anin yaɗa labarai, Mr. Femi Adesina, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a safiyar Litinin.

A cewar Adesina, taron wanda na haɗin gwiwa ne tsakanin Firam Ministan Birtaniya da Shugaban Ƙasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ana sa ran ya haɗa kawunan shugabannin ƙasashen duniya da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki har ma da shugabannin matasa, kuma zai ba da damar tattaunawar ƙawance a tsakanin mahalarta kan abin da ya shafi fannonin ilimin ƙasashensu tare da musayar ra’ayoyi.

“Taron zai bai wa shugabannin wata dama ta yin alƙawarin tallafa wa shirin GPE na tsawon shekaru biyar don taimakawa wajen bunƙasa sha’nin ilimi na ƙasashe kimanin 90,” in ji Adesina.

Daga cikin batutuwan da za a tattauna yayin taron kamar yadda sanarwar ta nuna, har da abin da ya shafin ilimin ‘ya’ya mata da kuma yadda za a zuba kuɗaɗe domin cigaban harkokin ilimi a ƙasashen da lamarin ya shafa nan da shekaru biyar masu zuwa.

Kazalika, Adesina ya ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai yi amfani da wannan dama wajen tattaunawar ƙawance tare da Firam Ministan Birtaniya, Boris Johnson.

Tare da cewa, “Bayan kammala taron Buhari zai shafe ‘yan kwanaki wajen duba lafiyarsa sannan ya komo gida ya zuwa mako na biyu na Agustan 2021.”

Buhari zai yi tafiyar ne bisa rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Ƙaramin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Maj. Gen. Babagana Monguno (rtd) da kuma Babban Daraktan Cibiyar Tattara Bayanan Sirri na Ƙasa, Amb. Ahmed Rufai Abubakar da sauransu.

Idan dai za a iya tunawa, kwanakin baya sai da Shugaba Buhari ya shirya tafiya Landon don duba lafiyarsa amma daga bisani aka soke tafiyar.