An tsawaita wa’adin shirin sadar da lambar shaidar ɗan ƙasa da layukan sadarwa zuwa Oktoba

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa’adin shirin shigar da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) cikin bayanan mallakar layin waya (SIM) ya zuwa 31 ga Oktoban 2021.

Gwamnati ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun manyan jami’ai biyu, wato Dr. Ikechukwu Ainde na Hukumar Sadarwa ta Nijeriya da kuma Mr Kayode Adegoke na Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin tsawaita wa’adin shirin ne sakamakon buƙatar hakan da masu ruwa da tsaki suka nuna domin bai wa shirin damar kaiwa ga jama’ar da ke gefen birane, baƙi mazauna ƙasa da kuma magance matsalar ƙarancin mallakar lambar NIN a makarantu da asibitoci.

Haka nan, sanarwar ta nuna auna yadda shirin ke gudana a yanzu domin sanin irin cigaban da aka samu na daga cikin dalilan da suka haifar da tsawaita wa’adin.

A cewar sanarwa, ya zuwa 24 ga Yulin 2021 akwai hanyoi sama da 5,500 a ciki da wajen ƙasa na gudanar da shirin wanda a cewarta hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa wa jama’a mallakar lambar NIN da kuma shigar da ita cikin bayanan SIM.

Ta qara da cewa, gwamnatin Shugaba Buhari ta ɗauki matakin tsawaita wa’adin shirin ne domin bai wa ‘yan ƙasa da ke gida da waje damar mallakar NIN tare da shigar da ita cikin bayanan layukansu na sadarwa, don haka ta ce akwai ‘yan ƙasa su ci moriyar wannan dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *