Hukumar DSS ta yi ram da Baffa Hotoro

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jami’an tsaron farin kaya na DSS a Kano sun cafke matashin nan Baffa Hotoro da ake zargi da yin sakin baki ga Manzon Tsira (S.A.W)

Tun a watan azumin da ya gabata ne dai Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa an kama matashin amma daga bisani Baffan ya fito a bidiyo ya musanta hakan, inda ya ce yana Saudiyya aikin Umara.

Amma a ranar Alhamis hukumar DSS a Kano ta tabbatar wa da gidan Radio Freedom Kano cewa suna tsare da Baffa Hotoro.