Hukumar NDE ta horas da mata 130 kan sarrafa tsirrai da ‘ya’yan itatuwa a Bauchi

Daga MU’AZU HARDAWA a Bauchi

Hukumar Samar da Aikin Yi ta Ƙasa (National Directorate of Employment), ta horas da mata 130 ilimin sarrafa tsirrai da ‘ya’yan itatuwa yadda za su yi tasiri wajen inganta rayuwa da lafiyar bil Adama.

Malam Aliyu Lawal Yaya, Daraktan hukumar ta NDE a Jihar Bauchi, shine ya bayyana haka lokacin taron yaye ɗaliban wanda ya gudana a harabar ofishin NDE da ke Bauchi.

Ya ce an karantar da ɗaliban da suka ƙunshi ‘yan mata da matan aure yadda za su gyara tsirrai da ‘ya’yan itatuwa kamar namijin goro da ciyayi da su habbatus sauda da sauransu, yadda za a riqa amfani da su don inganta lafiya ko rage ƙiba da sauran dabaru.

Bayan haka an ilmantar da su yadda ake rinin kaya da ɗaurinsu goggoro da kuma dabarun kwalliya a gida da sarrafa abinci da sauransu.

Aliyu Lawan Yaya ƙara da cewa tunda sun kammala za a duba ɗaliban da suka fi ƙwazo a tallafawa kowa da Naira dubu 25 don su sayi kayan aiki su ci gaba da sana’ar yadda suma za su koya wa wasu.

A yayin taron bitar na tsawon kwanaki biyar an basu abinci da kuɗin abin hawa da kuma kayan da ake amfani da su wajen koyarwa daga bisani kuma aka ba su takardun shaidar kammala karɓar horon don su ci gaba da koyar da wasu.

Harwa yau Malam Aliyu Lawal Yaya ya buƙaci ɗaliban su maida hankali wajen koyon ayyukan da aka ilmantar da su don su amfana su ilmantar da wasu, inda ya ce ɗaya daga cikin matan da ta koyar da su ta kashe Naira dubu 180 a Abuja kafin aka koyar da ita ilmin sarrafa tsirrai da itatuwa don amfanar da jikin ɗan adam, kuma yanzu aka ɗauke ta don ta koyar da su wannan ilmi saboda su amfana yadda ko a gidan aure za su taimaki kan su ba sai sun jira namiji ya musu wasu abubuwan ba.