Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da aka yi kan hanyoyin ruwa – Kwamishina

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Kano ta ce ta kafa wani kwamiti da zai gaggauta yin nazari da magance yawan ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama ke haifar wa a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Kano.

Ya ce gwamnati ta damu da irin ambaliyar ruwan da ke faruwa a jihar, musamman a cikin birni.

Ya ce kwamitin zai ɗauki nauyin duba titina, kwatoci da kwalbati da su ka lalace kuma su ke toshe magudnan ruwa domin a gyara, ko kuma a gina sababbi.

Ya ƙara da cewa kwamitin zai bi duk wasu gine-gine da a ka yi a kan hanyoyin ruwa da su ke haifar da ambaliya domin rushe su.

Kwamishinan ya kuma nuna rashin jin daɗi da kuma jajenta wa waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwan ya shafa.

Garba ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati za ta tashi tsaye wajen kawo ƙarshen matsalar cikin lokaci ƙanƙani.