An samu ƙaruwar satar ɗanyen mai cikin wata biyar a Nijeriya – NNPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Kamfanin Mai na Nijeriya NNPC, Malam Mele Kyari ya bayyana cewa an samu ƙaruwar satar ɗanyen mai a Nijeriya cikin watanni biyar, kamar yadda ya faɗa ranar Talata a Abuja, inda ya ce jami’an tsaron ƙasar sun gano aƙalla wurare 295 da aka fasa bututun don satar man a cikin tafiyar kilomita 200.

Ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a Fadar Shugaban ƙasar. A cewar Mele Kyari an kama mutane 122 da hannu a satar man tsakanin watan Afrilun bana da wannan watan na Agusta da ake ciki kaɗai.

Shugaban Kamfanin na NNPC ya ce haka ma jami’an tsaron sun gano haramtattun rumbunan adana ɗanyen mai 344 da tukwanen tafasa shi 355 da tankuna 759 da manyan motoci 37 da kuma jiragen ruwa 450 da ɓarayin man ke amfani da su wajen safarar man a yankin Neja Delta.

Ya ce hakan ya kawo nakasu ga yawan ɗanyen man da ƙasar ke samarwa a kowace rana; kuma idan aka tattara yawan man da ake asara sakamakon hakan zai kai ganga dubu 700 a rana.

Sai dai ya ce asarar gangar ɗanyen mai 700 da ƙasar ke yi a kowace rana ba ma ita ce matsala ba kamar lalacewar muhalli ke yi sakamakon aikace-aikacen masu satar ɗanyen man da kuma ƙoƙarin tace shi a haramce.

Da yake amsa tambaya dangane da ƙaruwar farashin mai da ake samu a ƙasar, Malam Mele Kyari ya yi wa ‘yan ƙasar albishir cewa mai zai wadata a ƙasar nan da tsakiyar shekara mai zuwa.

Nijeriya dai ita ce ƙasar da tafi kowacce fitar da ɗanyen mai a kasuwannin duniya a nahiyar Afrika, sai dai kuma takan kashe maƙudan kuɗaɗe wajen shigo da tataccen man da ake amfani da shi a cikin ƙasar saboda lalacewar matatun man ƙasar.