NIMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin Arewa biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET ta yi hasashen fuskantar ƙaƙƙarfan ruwan sama na tsawon kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa a wasu jihohin arewacin ƙasar 5, da kuma birnin Abuja, fadar gwamnatin Nijeriya.

Cikin rahoton hasashen yanayin da hukumar ta NIMET ta fitar, ta ce jihohin da za su fuskanci wannan ruwa na tsawon kwanaki 4 ba tare da ƙaƙƙautawa ba sun haɗa da Kaduna, Neja, Bauchi, Filato da kuma Jihar Nasarawa, baya ga birnin tarayyar ƙasar.

Rahoton na NIMET ya kuma yi hasashen fuskantar madaidaicin ruwan sama a wasu jihohin Nijeriya daga Kudanci da Arewaci da suka haɗa da, Kwara da Oyo da Kogi da Ekiti da Ondo baya da Sakkwato da Katsina da Zamfara.

Sauran jihohin da za su fuskanci mamakon ruwan sun haɗa da Kebbi da Kano da Jigawa da Yobe da Borno da Gombe da Adamawa da Taraba da Benuwai da Kiros Ribas da Akwa Ibom kana Ebonyi da Inugu da Abiya da Imo da Anambara da Ribas da Edo da kuma Jihar Delta.

Hukumar ta NIMET ta buƙaci ɗaukar matakan gaggawa don kauce wa fuskantar ambaliya musamman la’akari da cewa dukkanin jihohin da ta lissafa kama daga waɗanda za su fuskanci mamakon ruwan da waɗanda za su fuskanci madaidaici da kuma ƙaƙƙarfa, kowannensu zai zo da ƙaƙƙarfar iska.