Halin ha’ula’i da makarantar Turaki da ke cikin birnin Sakkwato ke ciki

…Mun bada umarnin kawo ƙarshen matsalar cikin gaggawa, cewar Shugaban SUBEB

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Makarantar ta Turaki dai na ɗaya daga cikin makarantun firamari a Sakkwato dake da daɗaɗɗen tarihi kasantuwar bayanai sun nunar da cewa an kafata ne tun a lokacin mulkin gwamnan soji na wancan lokacin Gado Nasko kimanin shekaru 40 da suka gabata.

Duk da daɗaɗɗen tarihin da makarantar firamarin ke da halin rashin magudanun ruwa dake damun makarantar ke fuskanta na cigaba da zama wani babban ƙalubale ga muhallin karatu ga ɗaliban makarantar dake karatu a ciki.

Manhaja ta samu damar kai ziyara a makarantar domin gane ma idonta halin da makarantar ke ciki, inda ma ta zanta da wasu ɗalibai dake karatu a ciki.

Wata ɗaliba da ta bayyana sunan ta Lubabatu dake karatu a makarantar ta bayyana halin da makarantarsu ke ciki a matsayin abin damuwa matuƙa.

“Idan aka yi ruwa makarantar mu na cika ƙwarai da gaske, sannan idan muka shiga ciki kafin kai wa da azuzuwa sukan lalata mata kayan makaranta, don haka ne muke kira ga gwamnati da ta duba yuwar kawo mana ɗauki a wannan makarantar ta yadda ko an yi ruwa muka zo kayan mu ba sa lalacewa.”

Makarantar dai ta kasance mai daɗaɗɗen tarihi da ma yawan ɗalibai abinda ma ta ya sanya aka samar da ƙaramar sakandare lamarin da ya sanya sashen kansa fama da matsalar.

A cewar wata ɗalibar ƙaramar sakandirin Hauwa lamarin kan sanyasu zullumi a duk lokacin da aka yi ruwan sama suna cikin makarantar.

“Wata rana idan an yi ruwa muna jin tsoron yadda za mu koma gida, kuma duk kayan makarantarmu su lalace, suma malamai idan za subje koyar danmu sai sunbbi cikin ruwan, ga yara na wasa da ruwa ta yadda hakan ke ɗauke hankali daga karatu kuma gashi ruwan ba su da tsafta, ka ga akwai fargabar iya kamuwa da cuta kenan don haka a taimaka mana a gyara mana makarantar mu don Allah.”

Da take zantawa da Manhaja shugabar ƙaramar sakandirin ta Turaki Malama Hadiza Shehu Abdullahi ta ta’allaƙa lamarin cikar makarantar da ruwa da ruwan sama kama da bakin ƙwarya da ake samun kwanan nan a wasu yankunan Arewacin ƙasar nan.

“Abin da ya kawo wanann matsalar shi ne rashin magudanun ruwa da ruwan dake harabar makarantar za su riƙa zurarewa a duk lokacin da aka yi ruwan sama ka ga dole a samu a wannan matsalar,” inji ta.

Duk da a cewar wasu mazauna unguwar matsalar ta haura shekara ɗaya da soma fuskantar matsalar, amma a cewar shugabar makarantar a bana ne kawai lamarin ya fi ta’azzara.

“Gaskiya bana ne matsalar ta fi ƙamari, kuma ina ganin idan aka samu hanyar da ruwan zai riƙa fita zai rage yawan kwantawarsa anan kamar yanda kuke gani, kuma mun sha rubuta ƙorafi da kaiwa gwamnati amma lamarin shiru da yake gwamnati abubuwa sun mata yawa, muna fatar dai ƙorafin da muka kai za a samar da mafita dama gyara a kai.”

Sai dai lokacin da Manhaja ta nemi jin ta bakin hukumar ilimi bai ɗaya ta jihar Sakkwato kan lamarin, daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Kabiru Aliyu ya buƙaci wakilin namu da ya koma a makarantar, domin jagororin hukumar na tattaunawa kan batun.

Sa’o’i ƙalilan da yin ayarin shugaban ya dira a makarantar firamare, inda ya zaga wajen lamarin ke addaba a cikin makarantar, inda ma wakilin namu Aminu Amanawa ya tambayi shugaban hukumar Altine Shehu Kajiji kan ko wane mataki suke ɗauka domin magance matsalar?

Shugaban ya bayyana cewa da dudduba matsalar da suka yi za su yi wani abu akai, duk kuwa da cewa al’umma ita ma na da rawar da ya kamata a ce ta taka akai.

“Gaskiya na ji yadda matsalar take shi ya sa na janyo babban sakataren wannan ma’aikatar, da daraktoci na domin mu duba mu ga mene ne ke faruwa, to gaskiyar lamari mun duba mun ga cewa an samu toshewar hanyar da ya kamata a ce ruwan ya wuce, kuma ka san muna a watan Agusta ne watan ruwa, kuma ina ga su hukumar makaranta da a ce sun duba sun doke wajen da lamarin ya toshe domin wani hoɓɓasa ko kuma ƙungiyar iyayen yara da malamai na makaranta, akwai ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai da sun tallafa da lamarin bai kawo hakan ba.

“Ba da daɗewa ba ma mun ba irin ƙungiyoyin nan Naira 100,000 ko wanen su, su yi amfani da su mana su ƙara sai a magance matsalar ba sai ma mun sani ba, ya kamata a ce al’umma ta san cewa kula da makaranta da ilimi ba wai haƙƙin mune kawai ba, suma iyaye na da nasu haƙƙin, yanzu misalin idan irin haka ya faru a gidajen mu, bama kwana sai mun fitar da ruwan daga ciki, to me ya sa bama yin haka a makaranta ita mai ai amfaninmu ne,” inji shi.

Bisa wannan ne ya sha alwashin hukumar na magance matsalar bada lokaci ba.

“Na bada umarni ga daraktan tsare-tsare namu da ya duba domin a ɗauki matakin kawo ƙarshen wannan matsalar.”

Makarantar firamarin Turaki da aka samar fiye da shekaru 40 da suka gabata dai na da sama da ɗalibai dubu biyar dake karatu a cikinta, baya ga sashen ƙaramar sakandaren da aka samar a baya-bayan nan.