Hukumomin Nijeriya sun kama shugaban al’ummar Falasɗinawa mazauna Nijeriya a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jami’an tsaron Nijeriya sun kama shugaban al’ummar Falasɗinawa a Nijeriya, Ramzy Abu Ibrahim a Abuja ranar Juma’a.

Wani ɗan uwa ya shaida wa SaharaReporters cewa jami’an sun kama Abu Ibrahim daga gidansa da ke Babban Birnin Tarayya (FCT), kuma har yanzu ba a sanar da iyalan inda aka kaisu ko kuma dalilin tsarewarsa ba.

Jami’an da suka bayyana kansu a matsayin na anti-terrorism sƙuad, a cewar ‘yan uwansa.

Jami’i a ofishin jakadancin Falasɗinawa da ke Abuja ya tabbatar da cewa suna da masaniya kan lamarin, amma har yanzu suna ƙoƙarin samun cikakkun bayanai.

“Eh, mun ji game da kama shi da aka yi kuma muna ƙoƙarin tantance bayanan,” inji jami’in.

Abu Ibrahim ya daɗe yana zaune a Nijeriya kuma an sha bayyana shi a jaridun ƙasar da kuma ta bakin fitattun mutane a matsayin shugaban al’ummar Falasdinawa a Nijeriya.

‘Yan uwansa sun ce akwai yiwuwar kama sa ba ta rasa nasaba da goyon bayansa na baya-bayan nan kan maganar hare-haren da ake kai wa ‘yan jarida da fararen hula a Gaza. Manhaja ba ta iya tabbatar da wannan zargi ba.

Manhaja ta sha bayar da rahoto kan yaƙin Isra’ila da Gaza da yadda yake jefa fararen hula cikin halin kakanikayi, ciki har da ‘yan jarida. Masana da dama sun bayyana cewa Isra’ila na aikata kisan kare dangi (genocide) a Gaza, kuma Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ƙasa da ƙasa (ICC) ta bayyana Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a matsayin wanda ya aikata manyan laifukan yaƙi a Gaza.

A ranar Litinin, jaridun ƙasashen waje sun ruwaito cewa jiragen saman Isra’ila sun kai hari kan asibitin Nasser da ke Khan Younis, Gaza, inda aka kashe aƙalla mutane 15 zuwa 20, ciki har da ‘yan jarida da dama.

Waɗanda aka ce sun mutu sun haɗa da Hussam al-Masri (ma’aikacin Reuters), Mariam (Maryam) Dagga (’yar jarida mai zaman kanta da ke aiki da AP), da Mohammed Salama (na Al Jazeera), yayin da Hatem Khaled, ɗan jarida mai ɗaukar hoto na Reuters, ya jikkata. Hukumomi sun ce suna bincike.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin tsaro na Nijeriya ba su fitar da wata sanarwa game da kamun Mista Abu Ibrahim ko inda yake ba.

Manhaja ta tura tambaya ga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi, domin samun karin bayani, amma bai mayar da martani ba tukuna.

Haka kuma, Zakari Mijinyawa, mai magana da yawun Ofishin Mai Ba wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), bai samu ba. An kira wayarsa ta yi ta kururuwa, sannan saƙon tes da aka tura masa bai samu amsa ba.

By ukarofi