Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar sojin Nijeriya a ranar Juma’a ta yi nasarar ceto mutane 76 kuma mafi yawancinsu yara ne bayan hare-hare da ta kai ta sama maɓoyar ‘yan bindiga da ke Katsina.
Sai dai yaro ɗaya a cikinsu ya rasu.
Rudunar sojin saman Nijeriya ce ta kai wani samame a ranar Juma’a da yamma kan maɓoyar gungun ɗan ta’adda Babaro da ke tsaunin Pauwa, a garin ƙanƙara.
Wannan hare-hare martani ne na irin mummunan harin gungun ‘yan bindiga Gidan Mantau suka kai da sace mutane da dama.
Kwamishinan tsaro na cikin gida, Nasir Mu’azu, ne ya tabbatar da ƙwato mutane 76 da gungun ‘yan bindiga na Gidan Mantau suka yi.
Sai dai ya ce, akwai yaro ɗaya da ya rasu a lokacin fafatawar.
Mahukunta sun wallafa hotunan waɗanda aka tseratar wanda ya nuna mafi yawan waɗanda aka sace yara ne.
“Yan bindiga sun shafe tsawon shekaru suna addabar yankin Arewa maso yamma suna kuma kafa sansanoni a dazuka waɗanda daga nan suke kai hare-haren kan ƙauyuka da makarantu da manyan hanyoyi da yin garkuwa da mutane.
Mu’azu ya ce, wannan samame wani ɓangare ne na sabunta fatan da sauya dabarun “tarwatsa maɓoyar ‘yan ta’addan” domin kawo ƙarshen garkuwa da mutane da kashe-kashe da ke addabar al’umma.
Gwamnatin Katsina ta yaba wa jami’an tsaro tana mai jaddada goyon bayanta wajen ba da tallafin kayayyaki da bayanan sirri domin yaƙi da ta’addanci.
Ana kuma roƙon al’umma da su zama masu lura da ba da bayanai a kan lokaci domin tallafa wa irin wannan samame da ke ake kai wa ‘yan ta’adda.
