Huriyya Dauda Lawal ta ƙaddamar da gangami kan allurar rigakafin Polio a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Matar gwamnan Jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ƙaddamar da gangamin wayar da kan alu’umma a matakin jiha kan allurar rigakafi cutar shan Inna, Kyanda da sauran cutukan dake addabar musamman mata da yara ƙanana, domin ƙarfafa kiwon lafiya a matakin farko a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A cikin jawabinta a yayin taron da aka gudanar a cibiyar kula da lafiya matakin farko ta Dr. Karima da ke Gusau, Hajiya Huriyya ta ce, kiyaye lafiyar kowane yaro ta hanyar allurar rigakafi ta yau da kullun shine mafi muhimmanci ga gwamnatin jihar.

“Kowacce uwa tana son ɗanta yayi walwala, ya yi wasa, kuma ya girma cikin ƙarfi da hankali. Hakan na kasancewa ne idan an ɗauki matakan da suka dace wajen rainon su, domin in babu ƙoshin lafiya, makomar ya’yan mu za ta zama ba ta da tabbas”. Ta ce.

A cewarta, har yanzu akwai yara waɗanda ba su sami allurar rigakafin ba, tana mai lura da cewa manufofin kamfen ɗin na wannan shekara shine tabbatar da cewa yaran da basu samu allurar rigakafin an yi masu allurar rigakafin a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Uwar Gidan Gwamnan ta ƙaddamar da matan ƙananan hukumomi 14 a matsayin jakadunta, waɗanda ake kira Mama Ambassadors, don fara kamfen ɗin cikin sauƙi a jihar.

“Mun zo nan ne don yin magana game da wani abu mai sauƙi amma mai matuƙar muhimmanci don mu wayar da kan alu’umma musamman iyayen yara da su kiyaye kowane lafiyar ya’yansu ta hanyar yin rigakafi akai-akai”. Ta ce

“Jakadun mu, matan shugabannin ƙananan hukumomi 14, za su ɗauki wannan saƙon zuwa ga al’ummar su musamman yankunan karkara, kasancewa sunfi kusa da alummar yankunan Karkara.

Hajiya Huriyya ta buƙaci matan shugabannin ƙananan hukumomi da su tunatar da sauran iyaye mata da su kawo ‘ya’yansu don yin rigakafi, su halarci cibiyar kula da masu juna biyu da kuma ci gaba da tuntuɓar cibiyoyin lafiya a yankunansu.

Ta kuma buƙaci iyaye, shugabannin addinai, sarakuna da al’umma da su yi aiki tare don samun nasarar allurar rigakafin a jihar.

Ta kuma nuna cewa alluran rigakafin da ake bayarwa a cibiyar lafiya suna da aminci. Tana mai jaddada cewa an yi amfani da su a Najeriya da kuma duniya baki ɗaya tsawon shekaru da dama.

“Waɗannan alluran rigakafin suna kare ‘ya’yanmu daga cututtuka masu barazana ga rayuwa kamar kyanda, polio, mashaƙo da tetanus, don haka akwai buƙatar iyaye su bar ‘ya’yansu su yi allurar rigakafin a jihar” in ji ta.

Shima a nasa jawabin, shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara, Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ya yaba wa matar gwamnan kan wannan shiri, ya Kuma yi alƙawarin yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki don tabbatar da nasarar aikin rigakafin.

By ukarofi