‘Yan matan Kebbi: Tinubu na tare da ku a halin jimami – Shettima ga iyayen ɗaliban

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya tabbatar wa iyaye da iyalan ɗalibai mata da aka yi awon-gaba da su a makarantar Government Girls’ Comprehensive Secondary School, Maga, Jihar Kebbi cewa gwamnati za ta yi dukkan abinda ya dace wajen ganin an ceto ƴaƴansu.

Haka kuma, ya ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin jimami game da faruwar al’amarin mai ban takaici, lamarin da ya sa ya ɗage tafiyarsa ziyarar aiki zuwa ƙasashen waje.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaba Tinubu, yana mai cewa sace yaran bala’i ne akan dukkan al’ummar Nijeriya.

Ya ce, gwamnatin tarayya za ta raba dukkan kayayyakin da ƙasar ta mallaka yayin atisaye ceton domin tabbatar da waɗanda suka yi garkuwar da makasan Birtaniya Janar M. Uba a Borno sun fuskanci hukuncin doka.

“Raɗaɗin Kebbi raɗaɗin Nijeriya ne. Idan aka ɗauke ɗa ɗaya, kowane gida a ƙasar nan zai yi jimami”, inji Shettima.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya za ta tallafa wa iyalan Marigayi Janar Uba, marigayin mataimakin shugaban makarantar da na sauran waɗanda ƙungiyoyin ƴan ta’adda suka yi silar mutuwarsu.

Kazalika, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris na jihar, jagororin al’umma, sarakunan gargajiya, ƴan bijilante, ƙungiyoyin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki bisa nuna damuwa game da wannan al’amari mai cike da baƙin ciki da jimami.

By Babaji