Ina sane da halin da ku ke ciki – Buhari ga sojoji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bikin Ranar Sojoji a matsayin wani abin da ke ci gaba da bai wa ‘yan ƙasa kyakkyawar fata da ƙwarin gwiwa a hanƙoron su na rayuwa cikin zaman lafiya irin na al’ummar da ke rayuwa ƙarƙashin tsari na dimokraɗiyya.

Rundunar Sojin Nijeriya wacce ke da dogon tarihi na shekaru 185 da ta somo daga Turawan mulkin mallaka, ta taka rawa na musamman a yaƙin duniya na farko da na biyu da kuma yaƙin basasar haɗa kan Nijeriya.

Shugaba Buhari wanda Ministan Tsaro Bashir Magashi ya wakilce shi, ya ce gwamnatin sa na sane da irin nasarori da rundunar sojin Nijeriya ke samu na zuwa ne da irin nasa ƙalubale, domin wasu sojojin sun rasa rayukan su, wasu sun samu raunuka wasu kuma sun daɗe ba sa tare da iyalan su, inda ya buƙaci dakarun da su ƙara zage damtse wajen ɓullo da sabbin dabaru da salon ƙara tunkarar ƙalubalen tsaro.

“Ina so in tabbatar maku da cewa gwamnatin mu tana iyakacin ƙoƙarin ta na inganta rayuwa da jin daɗin ku, za mu ci gaba da samar maku da duk abubuwan da kuke bu}ata na jin daɗi.

A gefe guda kuma ina sane da duk ƙalubalen da rundunar soji ke fuskanta na kayan aiki da wadatattun kuɗaɗen kula da kayan aiki da horaswa da kuma tafiye-tafiye wanda suke shafar aikinku. Kamar yadda kuke gani gwamnatin mu tana kan ƙoƙari wajen magance duk waɗannan matsalolin domin tabbatar da muradun ‘yan ƙasa.”

Shugaban ƙasar ya ce “Na hori manya da ƙananan sojojin Nijeriya da su kasance masu ƙwazo da kuma nemo sabbin dabaru da hanyoyin da zai kai su ga nasara wajen yaƙi da ta’addancin da shi ne babbar matsalar Nijeriya a hanzu.”

Tun da farko cikin jawabin sa, Babban Hafsan Hafsoshin Nijeriya, Manjo-Janar Farouk Yahya ya yi bayani kan salsalar bikin.

Janar Yahaya ya ce duba da irin rawar da sojojin suka taka wajen kawo ƙarshen yaƙin ya sa aka keɓe irin ranar kowane shekara don bitar yanayi da halin da dakarun suke ciki a kuma tsara yadda za a tunkari gaba.

Bikin na ranar wanda aka ƙarƙare da lakcoci da kuma karrama rukunan sojoji da Hafsoshi ashirin da suka yi fice a fagen daga irinsu Magatakardar Makarantar da Hafsoshin soji ta NDA, Birgediya Janar Auwal Mamuda Gumel da a lokacin da yake Kwamandan wani Birged a Arewa maso-Gabas ya jagoranci fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram tare da haɗin gwiwar sojin Kamaru a wani farmaki mai take ‘Operation Rufe ƙofa’.