Shin da gaske ne Gwamnatin Buhari na zuba dukiya a harkokin tsaro?

Daga NASIR S. GWANGWAZO

A yanayin halin da Nijeriya ta tsinci kanta a ciki yanzu, ba kowa ne ya sani ko zai iya gane ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan sha’anin tsaro ba, saboda yadda ake ci gaba da samun tangarɗa da cikas wajen shawo kan lamarin tsaro, wanda ya addabi al’umma, amma ko babu komai, za a iya cewa, haƙiƙanin ta’addanci da Boko Haram ta miƙe ƙafa ta na yi a gwamnatin baya, yanzu ya zama tarihi.

A yanzu babu ƙaramar hukuma ko guda ɗaya a hannun Boko Haram, duk da cewa, gwamnatin baya ta sadar wa ƙungiyar ƙananan hukumomi 14 cur a ƙarƙashinta tana yin mulki yadda ta ga dama a cikinsu.

A yanzu ba a iya kawo harin boma-bomai Babban Birnin Tarayyar Abuja da kewayenta, kamar a Nyanya da makamantansu. A yanzu ba a kai hari manyan masallatan ƙasar, kamar Babban Masallacin Juma’a na Kano da makamantansu. A yanzu jami’ai a caji ofis-ofis na ’yan sanda su na iya miƙe ƙafa su dararrashe a ciki ba tare da fargabar kawo hari ba, har ma wasu na zargin wasu jami’ai da sharɓar barci a cikin caji ofis lokacin aiki, saboda lalaci. Wannan baccin dama ce, wacce a baya ba su da ita. A yanzu ana shiga kasuwanni a gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da fargabar tashin bom ba.

Eh, gaskiya ne cewa, har yanzu akwai ƙalubalen tsaro mai yawa, musamman idan aka yi la’karai da batun garkuwa da mutane da ya ɓullo kai, amma kamar Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bayyana, ainihin matsalar tsaron da ta janyo aka kafu da son kafuwar Gwamnatin Buhari a 2015, yanzu babu ita, illa dai sabuwa da ta bayyana, wato garkuwa da mutane.

Idan za a iya tunwa, ɗaya daga cikin maƙasudin da za a iya cewa, ya janyo wa gwamnatin Jam’iyyar PDP a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, faɗuwa a Babban Zaɓen 2015 da aka gudanar a Nijeriya shine tabbas dalilin tsaro. Gwamnatin PDP da Shugaban Ƙasarta a wancan lokaci ana ganin ba su taka rawar da ta kamata wajen shawo kan matsalar tsaro ba. Wannan ya bai wa Jam’iyyar APC da ɗan takararta kuma Shugaban Ƙasa a yanzu, Muhammadu Buhari, cikakkiyar damar gudanar da yaƙin neman zaɓe ta hanyar caccakar gwamnatin PDP da kuma fito da aibunta ƙarara.

Don haka duk ɗan Nijeriya ya na sa ran idan APC da Shugaba Buhari suka kafa gwamnati za su kawo ƙarashen matsalar tsaro ɗungurungum a Nijeriya. Ita kanta APC da Shugaba Buhari sun san da wannan. Saboda haka tun daga lokacin da gwamnatin ta kafu, Shugaba Buhari ya mayar da hankali matuƙa gaya wajen ƙoƙarin tabbatar da cewa, gwamnatinsa ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin ƙasar, musamman ma yankin Arewa ko Arewa maso Gabas, inda balahirar Boko Haram ta fi ta’azzara.

Ko kun san cewa, a ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi na tabbatar da kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar a bayan zuwan gwamnatin ne har Rundunar Sojoji ta samu sukunin ƙera motocin yaƙi na ƙashin kanta a shekara ta 2017? Haka nan kuma ta ƙera jirgin yaƙi na Alpha Jet, wanda zai iya ɗaukar roket da bom ya harba tun a shekara ta 2016.

Ko kun san cewa, a cikin watan Maris na shekara ta 2021, a ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Buhari na fatattakar ’yan ƙungiyar Boko Haram, Gwamnatin Tarayya ta sayo wa Rundunar Sojin Ƙasa nagartattun motocin igwa-igwa da sauran kayan yaƙi daga Ƙasar Chana?

Wannan ya haɗa da tankoki 35, motocin ‘Typhoon MRAP’ guda 25, ‘Spartan’ guda 10 ta ɗaukar fasinjojin yaƙi, ‘Armoured Guard Booths’ guda 20, motar sharar hanyan yaƙi guda biyar, motocin ɗaukar dakarun mayaka guda 50 da mota ƙirar Bufalo guda 40 da sauransu.

Bugu da ƙari, ko kun san cewa, Gwamnatin Shugaba Buhari, ta hannun kamfaninta na Proforce, ta ƙera motar yaƙi mai suna MRAP a taƙaice, wacce za ta hutasshe da Nijeriya shigo da motocin yaƙi da ‘yan ta’adda?
Motar mai tsawon mita 3.4, injinta ya na da ƙarfin doki 400, wanda zai iya jure tashin fashewar bom ɗin da ya kai nauyin kilogiram 10. Ta na kuma da tankokin mai guda biyu masu ɗaukar litar mai 440, wanda hakan ke nufin za ta iya yin gudun kilomita 1,200 ba tare da ta buƙaci ƙarin man fetur ba. Motar ta MRAP kuma ta na da mazaunan taya masu iya tafiyar tsawon kilo mita 50 ko da tayar a fashe ta ke.

Wannan na nuni da cewa, gwamnati tana zuba maƙudan kuɗi a harkokin tsaro kenan kuma a shirye ta ke wajen yaƙi da ta’addanci a cikin gida ba tare da buƙatar shigo da motar hawa a fagen daga daga waje ba, domin motocin da ta ke iya ƙerawa sun fi inganci da ƙarfi kuma injinsu ba su ɗaukar zafi, kamar yadda kakakin soji ya furta, sannan shafin Ko Kun Sani NG da ke Manhajar Facebook ya wallafa! Da irin waɗannan bayanai za a iya cewa, tabbas Gwamnatin Tarayya ta cika alƙawarin ruguza Boko Haram, inda ta ƙarfi da yaji ta koma yaƙin sunƙuri kaɗai.

Eh, gaskiya ne za a iya jaddada cewa, da sauran rina a kaba ta fuskar masu sace mutane su na yin garkuwa da su, duk da irin zunzurutun kuɗin da Fadar Shugaban Ƙasa ke fitarwa ga fannin tsaro, inda ta kai ta kawo hatta Ministar Kuɗi Hajiya Zainab Ahmad, ta shaida wa Majalisar Dokoki cewa, Shugaba Buhari yana iya bayar da umarnin fitar da kuɗin ko-ta-kwana ga mayaƙan Nijeriya ba tare da jiran na cikin kasafin kuɗin ƙasa, don dai kawai a tabbatar da cewa, an yi nasara a yaƙi da ta’addanci.

Hakan ya tabbatar da cewa, Shugaban Ƙasar yana iya yin komai, don tabbatar da cewa, an samu nasarar abin da aka sanya a gaba. Abubuwan da ke kawo cikas kan hakan kuwa, musamman zargin cewa, akwai masu yin kwana da irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe da ake fitarwa, shi kuma wani abu ne daban, domin darasi ne, wanda za mu zauna a kansa nan gaba. Amma dai shi shugaban ya yi iyaka nasa! Sauran kuwa, mu ji tsoron Allah, mu damƙe amanar da ya ba mu bisa ainihin amana da sawaba da kuma salama!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *