Mazaje 16 da mata ba sa ƙauna!

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanku da da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Manhaja. A wannan mako, za mu kawo muku irin jerin mazajen da mata suke ƙyamar su haɗa inuwa ɗaya da su a zamantakewa ta aure. Duk da dai a ɗabi’ance ana ganin halitta da iya lafazin namiji yana rinjayar da soyayyarsa a zuciyar mace.

Amma akwai wasu abubuwa ko halayen da duk namiji mai su yakan zama abin ƙyama da gudu kuma a wajen mace. Waɗanda ko ƙwarewar namiji wajen kalaman jan hankalin ba za su iya tasiri wajen kawar da hakan ba. Sai dai ta zauna da shi don waau dalilai ba wai don tana so ko ganin girmansa ba. Wa]annan mazaje sun haɗa da:

  1. Namiji mai mita: Wannan shi ne namijin da zance ba ya wucewa a wajensa. Ko laifi mace ta yi masa zai yi ta mita yana ƙorafi. Kuma ba shi da yafiya. Zance ko na shekara nawa ne ba ya mancewa. Duk ran da aka yi masa laifi sai ya tayar da zancen. Irin waɗannan mazan kuma ba su da godiya. Duk kyautatawar da mace ta yi musu a tsahon shekaru masu yawa, idan ta yi laifi ba zai mance ba. Sai ma ya riƙe na sharrin. Irin wa]annan mazaje sukan fice a ran mace har ta ji ba ta ganin girmansa ko na sisi.
  2. Namiji mafaɗaci: A duk cikin rukunin mata ba macen da take son namiji mai tsananin fushi. Kodayake namiji mai fushi yana burge wasu matan idan suna kallonsa a matsayin tauraron fim ko na wani littafi da ake karantawa. Amma a zahirin gaskiya, mata ba sa sonsa saboda idan ransa ya ɓaci zai iya gaya mata duk maganar da ya ga dama. Kuma zai iya har dukan mace. Kuma irin waɗannan suna jawowa mace ta mai da musu da martani har raini ya shiga tsakaninsu. Kuma komai za ta yi masa sai dai don ganin ido amma a bayan idonsa ba za ta masa biyayya ba.
  3. Namiji mai girman kai: Shi ma namiji mai girman kai, soja ne marmari daga nesa. Yakan ƙayatar da mata ne kawai a kan fuskar talabijin ko a cikin ƙagaggun labarai. Amma a zahirance zama da shi da wahalar gaske. Mutum ne wanda bai karɓar laifinsa ko kaɗan ballantana a sa ran zai gyara. Namiji mai girman kai da izza ba lallai ne ya girmama kowa na mace ba. Tun daga iyaye har dangi. Soyayyar nan ba zai iya nuna wa matarsa ba saboda a wajensa ya bu]e ƙofar raini tsakaninsu.
  4. Namiji mai ƙorafi: Mata ba sa son namiji mai ƙorafi wanda ba shi da kau da kai ko kaɗan. Kuma wanda ba shi da godiyar Allah. Shi kullum ba kau da kai a kan laifin mace komai ƙanmantarsa. Sai ya mance da alkhairin shekaru aru-aru a kan laifi ɗaya rak. Kuma hakan zai zaftare kaso mai yawa na sonsa a zuciyarta. Watarana ma sai a nemi son ma a rasa. Domin a ɗabi’ar ɗanadam yana son yabo kuma ba ya son gwasalewa.
  5. Namiji mai zargi: Namiji mai zargi ko mai tsananin kishi yana da wahalar zama. Shi zuciyarsa ba ta huta ba, abokiyar zamansa ma haka. Mata ba sa son namiji mai zargi ko kaɗan. Domin zargi alama ce ta rashin yarda. Kuma mace ba ta ƙaunar a ce yau mijinta bai yarda da ita ba. Namiji mai zargi ko motsi mace ta yi sai ya fassara shi da wani abun. Shi ya sa kullum suke a cikin sa-toka-sa-katsi tsakaninsa da matar. Don ba kowacce nmace ce za ta yarda a dinga zarginta da wasu mugayen ɗabi’u ba. Musamman idan ta san ba ta aikata laifin hakan ba.
  6. Namiji malalaci: Mata sun fi son namiji mai ƙwazo a kowanne ɓangare na rayuwar aure musamman wajen jajircewa don rufa musu asiri. Namiji malalaci mara sana’a mai barin mace da wahalar kanta ya saya wa kansa da kansa raini wajen matarsa. Domin iya ɗaukar nauyin iyali shi ne abu ma fi girma da miji zai nema wa kansa kwarjini. Wani ma har da ƙari da kyauta. Sai ka ga son su da tausayinsa sun ƙara shigewa zukatan matayensu. Kamar yadda rai ke son mai kyautata masa haka mata suke gudun mazan da ba sa kyautata musu. Kuma suke son mai son su wanda yake sauke haƙƙin da Allah ya ɗora masa nata da na yaranta.
  7. Soloɓiyon namiji: Duk da yadda mata suke tsananin son su ga mazajensu sun zama masu sauƙin kai, amma ba sa son ya ta’azzara har ya zama soloɓiyo. Mace a rayuwa ta ɗauki namiji garkuwa wanda zai ba ta kariya daga dukkan abubuwan da take tsoro. Mata ba sa son namiji ya zama kyanwar Lami. Wanda masu iya magana suke ce wa, ba cizo sannan kuma ba kama ɓera. Kuma sannan da zai zama soloɓiyon mara wayo a kanta ita kaɗai da da sauƙi. Amma ya zama wawa wajen kowa a dinga juya shi kamar waina ne abin ƙi.
  8. Ƙazamin namiji: Yawanci maza ba sa la’akari da cewa mata ma fa suna son ɗabi’ar tsafta daga abokan rayuwarsu. Sai ka ga maza ba sa mai da hankali a kan tsafta. To ya kamata su sani, mata ma sun fi son namiji fes-fes, mai wanka da kwalliya da shafa turare da sauransu.
  9. Namiji marowaci: jimillar dukkan matan Duniya ba wacce za ta so marowaci. Kowa yana son mai kyautata masa. Rowa tana daga cikin halayyar rashin kyautatawa. Haka kyauta ga mace makami ne mai ƙarfi wanda yake fasa zuciyar mace ya dasa mata sonka a ciki.
  10. Namiji mai son kai: Mata Allah ya halicce su da son a kula da su. Shi ya sa maza masu dabara suke amfani da wannan makami don ribatar zuciyar mace. Namiji mai son kai shi kuma kansa kaɗai ya sani. Ba ruwansa da ƙoƙarin faranta ran matarsa. Shi dai kansa kawai. Wani ko a abinci da sutura sai ya ba wa iyalinsa tazara. Ya yarda ya bar iyalinsa da yunwa shi in dai ya ci ba matsala. Wannan mutum zai rasa tausayi daga matarsa da yaransa. Lokacin da ƙarfinsa ya ƙare yake buƙatar tallafi daga gare su.
  11. Namiji mai sa ido: Namiji mai sa ido yana da matuƙar baƙin jini a wajen mata. Wani namijin a kan gidan zai sa mata ido. Komai take yi yana ankare. Wani kuma a kan samunta zai sa mata ido. Daga ta ɗan samu wani abu sai ya janye jikinsa a wasu abubuwan na hidimar gida da Allah ya ɗora masa. Galibi waɗannan mazan ba ka raba su da hassada da son kansu da rashin son cigaban matar.
  12. Mai ƙarfa-ƙarfa: Namiji mai ƙarfa-ƙarfa yana da matuƙar baƙin jini wajen mata. Shi ne wanda ba ya bari mace ta ba shi shawara a kan komai. Mafi yawan lokuta ma ya fi yanke hukunci ba tare da ya sani ba. Ko da a kan abinda ya shafe ta ne ko yaranta. Irin waɗannan mazaje su ne suke iya ba da ‘yarsu har su sa ranar aure uwar yarinyar ba ta ji labari ba. Irin waɗannan maza suna da rashin farin jini gurin mata. Domin mace duk da rauninta tana so a ɗauke ta da muhimmanci har ma a dinga shawara da ita a wasu abubuwan.
  13. Mai yawan buƙata: Ba kowacce mace ce ke son namiji mai yawan buƙata ba, saboda mata ba dukka ke da buƙatar da za ta yi ɗaya da ta mijin ba.
  14. Namiji maras alƙibla: Akwai mazan da basu da alƙibla sam. Irin waɗannan mazaje ba su da tsayayyen ra’ayi guda. Yau idan suka yi gabas, gobe sai su yi yamma. Jibi kuma a hari Kudu ko Arewa, Haka dai. Irin waɗannan maza suna da wuyar sha’ani da wuyar mu’amala ga mace.
  15. Namijin zari: Namiji mai zari shi ne ba ya tsayar da zuciyarsa a kan mace guda ɗaya sai ya yi ta hange-hange. Namijin zari ba zai taɓa wadatuwa da mace ba. Irin waɗannan mazan ko mace ɗari za su mallaka sai sun hango wata wacce za su ji ta fi birge shi fiye da waɗancan ɗarin. Kasancewar mata da kishi, sam ba sa iya jure rayuwa da namijin zari.
  16. Miskili: Duk mace tana son namiji miskili. Amma a cikin ƙagaggun labarai ko ta gan shi a kan hoto mai motsi na talabijin a cikin shirin wasan kwaikwayo. Amma zama da su akwai wahala domin yana da daɗin zama saboda bai cika magana doguwa ba. Sannan ba ya saka miki ido a kan harkokinki. Sai dai idan faɗa ya shiga tsakaninsa da matarsa abun ba kyau. Mace tana azabtuwa a hannunsa. Domin zai iya share tsahon lokaci da mace ba ya mata magana kuma abun sam ba zai dame shi ba. Haka idan ya ƙaurace wa mace sai dai ta sauke duk wani jan ajin mace ta lallshe shi. Don lallashi ba ya daga abubuwan da wannan mutum ya iya. Kuma yana dagewa wajen ɓoye soyayya. Zai iya jure soyyarsa don ya hukunta abokiyar rayuwarsa.

Don haka yan maza sai a dage a yi hattara, don ganin ba su faɗa cikin ajin waɗannan mazaje da kadararsu ba ta sayuwa a kasuwar mata.