Ina shan wahala saboda tsadar dizel – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya yi ƙorafi akan tsadar dizel da farashin abincin dabbobi da kuma farashin canji da yadda hakan ke shafar noman kifi a Nijeriya.

Obasanjo wanda manomin kifi ne ya ce yana cikin tasku saboda tsadar dizel, lamarin da ke kawo tsaiko ga noman kifinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Obasanjo ya yi wannan magana ne ranar Talata a Abeokuta da ke Jihar Ogun, a lokacin taron Ƙungiyar Manoman Kifi na yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya a cikin Ɗakin Karatun Obasanjo (OOPL).

Obasanjo ya bayyana cewa cigaba da tashin farashin dizel da kuma cigaba da ƙaruwar farashin abincin kifi zai hana manoman yin aikinsu, sai dai in har sun haɗa kai su amince da farashin da za su cigaba da barin su suna sana’ar.

Ya yi bayani yana cewa a halin yanzu farashin dizel 800 ne lita ɗaya, sannan samar da kilo ɗaya na kifi Naira 1,400 ne, kuma ya qara da cewa, idan har suna son samun riba, to ba za su iya sayar da kifi ƙasa da 1500, lamarin da ya sa su duk wani abu da ya yi ƙasa da haka zai jawo faɗuwa ne da asara.

Obasanjo ya ce: “Farashin dizel ya yi sama saboda yadda ake tafiyar da ƙasar nan ba yadda ya dace ba ne.

“Saboda haka idan haka ta faru, wasu daga cikinmu da muke buƙatar amfani da dizel domin noman kifi za mu yi asarar ne bakiɗaya, kuma a lokacin da hakan zai faru, ‘yan Nijeriya za su ci gaba da buƙatar cin kifi.

“Noman kifi zai gagara, sannan manoman da ke wajen Nijeriya za su ringa kawowa nan.

“Za ka rasa aikin yi, ka talauce. Saboda haka me ya kamata mu yi? Mu hada kai mu cigaba da raya noman kifi domin kula da buƙatun waɗanda su ke cin kifi da kuma masu noman kifin,” a cewarsa.