Ganduje ya bada umarnin rushe ginin filin gidan Sheikh Nasiru Kabara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin rushe wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a kusa da gidan Sheikh Nasiru Kabara da ke Unguwar Kabara a daren Litinin da ta gabata.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ne ya bada umarnin bayan bincike ya nuna cewa babu wani umarni a hukumance na yin ginin a filin wanda mallakin masarautar Kano ne.

Ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar KAROTA, Nabulisi Abubakar K/Na’isa ya fitar, ya ce shugaban hukumar ta KAROTA kuma shugaban kwamitin cire duk wani gini da ya saɓa da doka ya shaida wa al’umma cewa ba kamar yadda ake yaɗawa ba, gwamnatin Kano da Masarautar Kano ba ta da masaniya kan ginin.

Sanarwar ta cigaba da cewa yayin da ake ci gaba da bincike, Gwamna Ganduje ya bada umarnin rushe ginin gabaɗaya sannan ya amince a mayar da wurin wajen wasan yara yayin da ragowar filin za a dinga zikirin Ƙadiriyya a ciki.

Binciken da Manhaja ta gudanar ya nuna cewa ko a shekarar 2013 an fara gini a filin, inda ba tare da ɓata lokaci ba Marigayi mai Martaba Sarki Ado Bayero ya hana ginin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *