Yadda ɗan mai sayar da jarida ya zama zakara a makarantar kuɗi a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Wani yaro ɗan shekara 19 mai suna Abdulrahaman Iliya Hamman da ya kasance ɗan talaka da mahaifinsa ke sayar da jarida ya zama zakara a makarantar kuɗi ta Kanady Academy Gombe, inda ya yi wa ‘ya’yan masu kuɗi fintinkau ya kuma karvi kyaututtuka a kowanne ɓangare bayan kammala jarrabawar fita.

Da yake zantawa da wakilinmu a lokacin bikin yaye ɗalibai na makarantar, Abdurrahaman Iliya ya ce a matsayinsa na ɗan talaka ya samu kansa a cikin ‘ya’yan masu kuɗi kuma ya yi fice a cikin su wannan ba ƙaramin abun godiya bane ga Allah.

Ya ce yana cike da farin ciki ganin yadda a wannan rana ya samu kyaututtuka masu yawa kuma ya zama shi ne mafi hazaƙa daga cikin ɗalibai ‘overall best’ na ɗaliban da suka gama karatu su 32 a makarantar.

“Mahaifina talaka ne jarida yake sayarwa kuma yanzu harkar jaridar ma ta zama sai a hankali amma duk da haka bai gajiya ba ya yi ta kokarin sa wajen ganin nayi karatu a irin makarantar da ‘ya’yan masu kuɗi suke yi,” inji shi.

A cewarsa da yake ya fi ƙwarewa a ɓangaren kimiyya da lissafi ya ce fatansa ya zama injiniyan hanyoyi ko na gine-gine idan ya tafi jami’a.

Abdurrahaman ya ce ƙasar nan yanzu aiki yana wahala idan kai ba dan kowa bane, shi ya sa yake so ya samu hanyar dogaro da kan sa wanda ko ba gwamnati zai yi aiki ya kuma ɗauki wasu ma’aikata a ƙarƙashinsa.

A nasa ɓangaren Mahaifin Abdurrahaman Malam Iliya Hamman, ya ce yana cike da farin ciki marar adadi da kuma shauƙi na yadda a matsayin sa na Talaka dan sa ya kere sa’a a tsakanin ‘ya’yan masu kuɗi.

Malam Iliya, ya ce harkar sayar da jarida yanzu ta mutu ba kamar da ba amma da yake yana son dan ya yi karatu yana haɗawa da noma da kuma wasu buge-buge a gefe don ya samu hanyar biyan kuɗin karatun ɗan nasa.

Ya ce da farko yaron ya ɗan sa wasa a ransa duk da cewa yana da ilimi sanda ya haɗa shi da shugaban makarantar Mista J.B Ishaya, ya zama kamar uba a wajensa yana masa gargaɗi yana jan hankalinsa wajen karatu sannan ya cire wasan a ransa ya rungumi karatun da ya ke dama mai qoqarin gaske ne, inji shi.

Har ila yau ya sake gode wa Ishaya sannan ya jinjina wa hukumar makarantar ta Kanady Academy bisa irin tsarinsu na yadda suke karantar da yara a makarantar.

Malam Iliya ya ce ba zai gajiya ba zai cigaba da ɗaukar nauyin karatun xan nasa har zuwa jami’a.

Daga na sai ya shawarci iyaye da cewa su daure wajen tsayawa kan karatun ‘ya’yansu komai rashin kuɗinsu Allah zai taimake su, domin ilimi shi ne gadon da za su bar wa ‘ya’yansu ba dukiya ba.