Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Cibiyar Horas da Matasa Sana’o’in Dogaro da kai daban-daban wace ke samun talafin daga gidauniyar Dr. Rufai Mukhtar Ɗanmaje foundation da sauran masu kishin aluma a kano da ƙasa baki ɗaya yanzu haka ta samu nasarar hurara da matasa sama da dubu 17 sana
oi daban daban kamar ɗaukar hoto koyar da kwamfuta, ɗinki, koyar da aikin jarida da sauran sana`o’i.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kwamared Mukhtar Musa ‘Yankaba, babban jami’i mai kula da cibiyar a lokacin da yake jawabi yayin bikin yaye wasu ɗalibai kimanin 200 da wani bawan Allah ya ɗauki nauyinsu gayin wani biki da aka yi a ɗakin karatu na Murtala Muhammed da ke Kano a ƙarshen makon da ya gabata.
Kwamared Musa ‘Yankaba, ya ce suna yaba wa Alhaji Rufai Ɗanmaji saboda irin gudunmawarsa da ya ke bayarwa wanda a lokaci ƙanƙani ya ɗauki nauyin matasa kimanin dubu 15 wajen koyar da su sana’o’i wanda ba ƙaramin al’amari ba ne kuma akwai buƙatar mawadata da sauran jami’an gwamnati a kowane matakai su riqa ɗaukar matasa koyar da su sana`o’i kamar yadda Ɗanmaje da sauran wasu shugaban da suke yi.
Domin hakan shi ne zai samar da aikin yi tsanin matasa wanda zai bunƙasa tatalin arziƙin kano dama Najeriya kuma hanya ce ta bunƙasa tsaro da zaman lafiya a wannan lokaci abin farin ciki shi ne yadda wasu matasa da suka samu horon nan suka fara ɗaukar wasu matasa aiki ko kuma dogaro da kansu a wurare daban-daban.