Jama’a ku daina ganin laifin Buhari da Ganduje – Madugawa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Alhaji Salisu Madugawa, dattijo ɗan shekara 72 a duniya kuma shugaban Ƙungiyar Manoma ta Amana Farmers Association ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ya bayyana cewa cigaban Kano da aka samu a zamanin Gwamna Dr.

Abdullahi Umar Ganduje da kuma wasu matsaloli na rayuwa da ake samu dama haka rayuwa take akwai nasara akwai ƙalubale, don haka bai kamata mutanen Kano su riƙa maganganu ko ganin matsalar gwamnan Kano ba domin shi ɗan Adam ne zai iya yin daidai zai kuma iya yin akasin haka; don haka zage-zage ko maganganu marasa kan gado a cewarsa bai kamata ba, addu’a ya kamata kowa ya yi akan duk wasu matsaloli da aka gani sun gagara da tunanin ɗan Adam wannan shi ne ya kamata amma ba akasin haka ba.

Alhaji Salisu Madugawa ya bayyana haka ne lokacin da yake qarin haske kan matsalolin rayuwa da aka samu kai yanzu haka a Nijeriya ya ce dangane da matsalolin da aka samu kuwa a Nijeriya bai kamata a ɗaura wa mutum ɗaya ba kamata ya yi kowa ya tashi tsaye wajen ganin ya bada gudumawarsa ta cigaban Nijeriya ta ko wacce fuska.

Domin yanzu haka Nijeriya na buƙatar gudunmawar kowa da kowa ta ko wane fanni domun dama ƙasa ita kamar kan ɗaki ne sai an haɗa hanmnu wajen ciyar da ita gaba ako da yasuhe dan haka afahimtata a cewar Madugawa ba Buhari ba ne kawai mai laifi dai shi shugaba ne kuma shugaban Nijeriya ne ƙasa ce mai wuyar tafiyar da al’amura na mulki kuma dama shi mulki haka ko akasin haka dole shugaba za a ɗorawa amma dai mu zama masu kyakyawar fahimta da fatan alheri ga ƙasarmu.

A ƙarshe Madugawa ya roƙi shugaban ƙasa Muhammad Buhari kan ƙara jajircewa wajen agazawa harkar noma, tsaro da sauransu domun kowa abubun da suke faruwa na rashin sakewar manoma a wasu wurare a ƙasar nan abun tambaya ne ga alumar Najeriya, su waye ke kokarin kowo ma Nijeriya cikas ta famnin noma da sauran alumaran cigaban Najeriya wannan abun damuwa ne kuma wajibi ne ayi ƙoƙarin tabbatar da adalci a kowane mataki domun ba mu da wata qasa sai Nijeriya kuma kowa ɗanta ne da ya kamata ya taimaki ƙasar sa, indai shi ɗan Nijeriya ne mai kishinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *