
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ɗaukaka ƙarar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke wani sashi na sharuɗɗan da hukumar ta samar akan babban zaɓen 2027.
INEC ta buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja da ta jingine hukuncin Babbar Kotun, wanda ya sauya wa’adin da ta ba wa jam’iyyun siyasa na miƙa mata (INEC) jaddawalin rajistar mambobi gabanin zaɓen 2027.
A ‘yan kwanakin nan ne Mai Shari’a Muhammad Umar na Babbar Kotun da ke Abuja, ya soke sharuɗɗan da INEC ta bayar da ke umartar jam’iyyun da su miƙa jaddawalin zuwa ranar 10 ga watan Mayu a matsayin ƙa’idar shiga babban zaɓen.
Umarnin kotun ya biyo bayan wata ƙara ne da jam’iyyar YP (Youth Party) ta shigar na ƙalubalantar sahihancin sharuɗɗan da INEC ta sanya wa jam’iyyun.
Mai Shari’a Umar ya ce, INEC ba ta da ikon tsuke wa’adin da dokar zaɓe ta 2026 ta samar wa jam’iyyu na gudanar da harkokinsu.
Ya yi hukuncin cewa dokar zaɓe ta ba jam’iyyu har tsawon kwanaki 120 gabanin zaɓe na su miƙa dukkan wani bayani da ya shafi ‘yan takararsu.
Akan haka ne INEC ta lauyanta Alex Izinyon (SAN), a wata ƙara da ta shigar a ranar 25 ga Mayu, ta nemi Kotun Ɗaukaka Ƙarar da ta soke hukuncin Babbar Kotun tare da dakatar da aiwatar da shi.
