INEC ta saka ranar bai wa zaɓaɓɓun gwamnoni da ‘yan majalisun jiha takardar shaidar cin zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya, INEC, ta ce ta saka ranakun da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohin ƙasar da aka gudanar da zaɓen gwamna.

A wata sanarwar da hukumar INEC ɗin ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a na hukumar, Festus Okoye, ta ce sashe na 72 (1) na Dokar Zaɓen ƙasar ta 2022, ya ɗora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun ‘yan takara a cikin kwana 14 da yin zaɓen.

A kan haka ne hukumar ta ce ta saka ranar Laraba 29 ga watan Maris da kuma 31 ga watan na Maris a matsayin ranar da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓun gwamnoni da mataimakansu, tare kuma da ‘yan majalisun dokokin jihohi.

Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar cin zaɓen ne a harabar ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar.

Hukumar zaɓen ta ce kwamishinonin INEC na jihohi da ma’aikatan hukumar za su sanar da zaɓaɓɓun takamammiyar ranar da za su karɓi takardun shaidar.