Batun zubar da ciki: Babban Hafsan sojoji ya ƙaryata jaridar Reuters, ya ƙalubalance ta ta kawo hujja

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Hafsan Rundunar Sojin Nijeriya (COAS) Laftana Janar Farouk Yahaya ya ƙalubalanci jaridar Reuters ta ba da hujja a kan rahoton da ta take yaɗawa wanda a ciki take ikirarin cewa, an gudanar da zubar da ciki har guda 10,000, an yi kisan kiyashi na yara da dama da yake da alaƙa da cin zarafin jinsi ta hanyar jima’i da suka danganta shi da hukumar sojin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, COAS ya zo da ƙalubalen ne a yayin da yake ba da bayanin a gaban wani Kwamiti na musamman na Hukumar hana cin zarafin ɗan’adam na shirin yaqi da ta’addanci a Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda ya bayyana cewa, wannan a matsayin wani tsararren wasan kwaikwayo ne don vata nasarar sojojin a Arewa maso gabashin.

Da yake tsokaci game da rahoton da jaridar Reuters ta rawaito, Laftana Janar ɗin ya kada baki ya ce: “Wasu mutanen Allah ya yi musu baiwar iya tsara labari kamar a littafin ƙagaggun labarai, su dinga siffanta abinda ba su taɓa gani da idonsu ba, sun manta cewa, a hukumar sojoji in dai ka yi asarar harsashi ko guda ne sai an gurfanar da kai a kotu. Mu ba sojojin kasuwanci ba ne, mu ƙwararrun sojoji ne.

Ya ƙara da cewa, kuma hukumar sojoji suna samun nasara sosai, abinda ya sa kenan wasu da suka san ba za su iya mayar da hannun agogo baya ba, sai dai su yi hassada da ƙoƙarin ɓata suna.

A cewar sa, abinda waɗannan mutanen suka manta shi ne, rundunar sojin sun samu horaswa ta zama ƙwararru, kuma a cewar sa wataqila ba su san sojoji a ƙarƙashin gwamnatin Nijeriya suke ba, kuma ƙasarsu suke yi wa aiki ba? Sannan kuma a cewar sa, ya kamata su san sojoji ba kamar ‘yan Boko Haram suke ba, suna aikinsu ne cikin tsari da nagarta.

Ya ƙara da cewa, rundunar sojin Nijeriya ba su da wani muradi illa yaƙi da ta’addanci da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali don haka ba za su bar aikinsu mai mutunci ba, su vige da zubar da ciki har guda 10,000 da ‘yan Boko Haram suka yi.

A cewar sa, ba aikin hukumar sojojin ba ne kawar da ƙyamar da ake nuna wa irin waɗannan ‘ya’ya ba, don haka wannan abin dariya ne a cewar sa.

Haka a cewar sa, zancen cewa hukumar sojin tana sayen makamai don yaqi da ta’addanci ya kamata a ce Reuters su goya musu baya a kan haka, ba wai a dinga kawo wasu shawarwari ba na littafi waɗanda ba za su taɓa aiki a zahiri ba musamman a kan matsalar Arewa maso gabas ɗin.