Marafan Kaiama, Idris Muhammad ya rasu

Daga WANILINMU

Allah Ya yi wa Marafan Kaiama a Jihar Kwara, Alhaji Idris Muhammad Madugu, rasuwa.

Ya rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da rashin lafiya.

Salihu Ɗantata shi ne ya ba da sanarwar rasuwar a shafinsa na Facebook.

A halin rayuwarsa, marigayin tsohon ma’aikaci ne ƙarƙashin Gwamnatin Jihar Kwara, kafin daga baya ya yi titaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *