Oladipo Diya ya rasu yana da shekara 79

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a gwamnatin marigayi Sani Abacha, Lt-General Donaldson Oladipo Diya, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 79.

Ɗan marigayin, Prince Oyesinmilola Diya, shi ne ya ba da sanarwar rassuwar mahaifin nasa cikin sanarwar da ya fitar da safiyar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce, “A madadin ahalin Diya na gida da waje, muna sanar da rasuwar maigidanmu, mahaifinmu, kakanmu, ɗan uwanmu, wato Lt- General Donaldson Oladipo Oyeyinka Diya (mai murabus) GCON, LLB, BL, PSC, FSS, mni.”

Marigayi Oladipo diya

Sanarwar ta nuna marigayin ya cika ne ranar Lahadi, inda iyalansa suka buƙaci a taya su da addu’a a wannan lokaci jimami.

Iyalan marigayin sun ce za a sanar da jama’a game da halin da ake ciki ba da jinawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *