Iyaye da malamai sun shiga damuwa bayan da Gwamna Inuwa ya kulle wasu makarantun jinya a Gombe

Daga MOHAMMED ALI a Gombe

Iyayen dubban ɗaliban makarantun koyon kiwon lafiya, wato Schools of Health a Jihar Gombe, yanzu haka, suna cikin wani hali na damuwa, biyo bayan rurrufe makarantun kusan 20 dake faɗin Jihar, waɗanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bada umarnin a rufesu tun watanni kusan huɗu da suka wuce.

Binciken da muka gudunar ya nuna cewa, makarantun suna nan kango, cike da ƙwari da shara, a wasu ma, ko masu gadi babu, tunda duk ƙofofin shiga harabar makarantun a garƙame suke kam-kam, kulle da makullai. Ko me ya jawo dalilin rufe waɗannan makarantun masu muhimmanci ga ɗalibai?

A cewar ɗaya daga cikin masu irin wannan makarantar da lamarin ya shafa, kuma wanda ba ya son a faɗi sunan shi, gwamnati ce ta yi zargin cewa ba su da sahihin abubuwan da suka kamata da za su samu damar bada horo a irin wannan makarantar ta koyon ilimin kiwon lafiya, don haka ta rurrufe su.

Amma kuma su masu makarantun, sun musanta wannan zargi, suna masu cewa, tun kafin su buɗe makarantun, sai da suka bi duk sharuɗɗan da suka kamata tun daga Hukumar Ilmi ta Jiha har zuwa ta Tarayya, kuma duk Hukumomin Ilmin sun gamsu, kuma suka basu izinin ɗibar ɗalibai masu ilimi da masu sha’awar koyon darasi a kan kiwon lafiya da bincike-bincike akan shi.

“Ai babu yadda za a ba mu izinin gudanar da wannan fannin ilmi idan ba mu da sharuɗɗan yin haka. Kuma yaya sai bayan shekaru muna tafiyar da harkar mu, a ce yanzu ne gwamnati za ta san ba mu cika sharuɗɗan ba, ta kukkulle mana makarantu?, kukan masu makarantun kenan.

Wani malami dake koyarwa a wata makaranta da abin ta shafa, wanda bai faɗi sunan shi ba, ya shaida cewa, al’amarin ya zo musu a bazata kuma abin da gwamnati ta yi, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, yana ƙarawa da cewa, “sam, wannan abu bai yi daidai ba. Yanzu haka, an bar yara kara zube, kuma idan ba a yi hankali ba, za su (ɗalibai) zama zauna-gari-banza, kuma abun damuwa ne. Don haka, gwamnati ta buɗe mana makarantunmu, malamai su cigaba da koyar da ɗaliban.”

A ɓangare guda, wani uba mai yara uku a ɗaya daga cikin makarantun, Malam Muhammad Giɗaɗo, shi kuka ya yi ga gwamnan, da ya tausaya musu, da su da malaman makarantun da masu makarantun da ɗaliban makarantun, musamman yanzu da jarrabawa na gab da zuwa.

Haka shi ma wani mahaifin wata ɗaliba, Malam Sani Rilwan Bajoga, roko ya yi ga gwamnan da ya dube su da idon rahama, ya buɗe makarantun.

Sai dai kuma, bincike ya nuna cewa, akwai makarantu biyu ko uku da gwamnatin bata rufe su ba, abin da ya jawo cece-kuce da zarge-zargen cewa, su makarantun ta wasu, “manyan mutane ne waɗanda kuma suke kusa da gwamnati,” a cewarsu, abin akwai siyasa a ciki don dai a baiwa waɗannan makarantu ukun gudanar da duk abin da suka ga dama, ko ta wajen kuɗin makaranta, su kuma mamaye ko’ina suna gudanar da harkokinsu a makarantun su kaɗai, ba tare da wasu kishiyoyi ba.

Koma mene ne, masu makarantun da rufewar ta shafa, da malamansu da iyaye da ɗaliban makarantun, sun zuba idanu su ga ko gwamnati za ta saurari koke-kokensu ta bubbuɗe musu makarantunsu.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin gwamnati ta hannun mai bata shawara akan labarai, bai yi nasara ba saboda bai amsa kiran waya da aka yi mishi ba.