2023: Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya ya ƙaddamar da bai wa jami’ansa horo a Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Maiduguri

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Usman Alƙali ya ƙaddamar da horas da jami’an ‘yan sanda, wanda ya ƙunshi samar da tsaro a lokutan manyan zaɓukan 2023 mai zuwa, wanda ya haɗa da wani taron bita ta hanyar haɗin gwiwa da masana da sauran ɓangarorin hukumomin tsaron a jihar Borno.

Kamar yadda ajandar taron ta nuna, wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen da take aiwatarwa wajen tabbatar da ganin zaɓukan sun gudana cikin tsanaki, ba tare da samun wata tangarɗa ba a babban zaɓe mai zuwa.

A makonnin da suka gabata ne Sufeto Janar na ‘yan sandan ya gudanar da wani taron ƙara wa juna sani na ƙasa baki ɗaya a Abuja, wanda ya ayyana cewa, “wannan horo ne a ƙoƙarin da muke yi na musamman wanda zai ƙara wa ƙwarin gwiwa ga jami’an ‘yan sanda wajen ganin sun sun gudanar da ayyukansu na tsaro a lokutan zaɓe don a samu sahihin zaɓe mai cike da kwanciyar hankali.”

Taron na yini ɗaya ranar Litinin a masaukin baƙi na Pinnacle Hotel dake Maiduguri tare da haɗin gwiwar kamfanin tsaro na Solar Security and Consult Company. Taron mai taken: “Zaɓen 2023 da inganta tsaro ga ƙasa don samar da ingantaccen tsarin zaɓe a Nijeriya, da tabbatar da tsaro da oda.” Wanda kimanin wakilai a shiyoyi shida a faɗin ƙasar nan.

A jawabin tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sandan Nijeriya, kuma jami’in da yake kula da bayar da horon, ga jami’an ‘yan sandan jihar Borno, mahalarta taron waɗanda suka haɗa da jami’an Hukumar NDLEA, ƙungiyar lauyoyin Nijeriya ta NBA, ƙungiyoyin farar hula, ‘yan jaridu da sauran su jama’a, Mista Solomon Arase inda ya buƙaci su rinƙa tausasa zukata tare da bai wa kowa dama da ‘yanci a mu’amalar yau da kullum da juna a lokacin musayar ra’ayi, a madadin Sufeto Janar na ‘Yan sandan Nijeriya.

Arase ya ce, ana sa ran taron zai tavo batutuwa biyar masu muhimmanci bayan horon waɗanda suka ƙunshi; samun haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen samar da ingantaccen tsari a lokacin babban zaɓen 2023 da sauran ayyukan tsaro na haɗin gwiwa; Ingantacciyar hanyar samar da sahihan bayanai tsakanin jami’an tsaro a lokutan zaɓe, samar da daidaitattun matakan gudanar da ayyukan tsaro a lokacin zaɓen 2023.

“Har wala yau kuma, mu na sa ran wannan takardar bayan taron za ta yi aiki a matsayin tabbataccen kundi ga dukkan hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen Nijeriya; tare da auna matsayin da barazanar tsaro a lokutan manyan zaɓuka, ƙoƙarin gano tushen su da kuma takamaiman hanyoyin da wasu ke bi wajen gudanar da su a matakai daban-daban. Sannan da ɗaukar matakan hanzari wajen daƙile aikata laifukan zaɓe da barazanar su.”

A nashi ɓangaren, Gwamna Babagana Zulum wanda ya samu wakilcin babban sakatare kuma babban lauyan ma’aikatar shari’a Isa Izge, ya yaba wa Sufeto Janar na ‘Yan sandan Nijeriya, IGP Alkali bisa wannan gagarumin shiri, wanda zai taimaka wajen samun sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali mai cike da tsafta a 2023.

A nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, CP Abdul Umar, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, DCP Garba Dugum, wanda ya fara da yaba wa IGP Alkali na shirya taron bitar, domin a cewarsa, “taro ne wanda ya zo lokacin da ya dace. Wanda hakan zai bada dama ga hukumomin tsaro su yi tunani tare da tattauna sabbin hanyoyin da za a bi don tabbatar da sahihin zaɓe a jihar da ƙasa baki ɗaya.”