An cimma daidaito a taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministocin FOCAC na 8

Daga CMG HAUSA

A yayin taron manema labaru da aka gudanar a yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya yi bayani game da sakamakon da aka cimma a taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministocin dandalin tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka FOCAC na 8, inda ya bayyana cewa, yanayin taron ya yi kyau kuma yana da ma’ana sosai. Ɓangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi da cimma daidaito kan yadda za a aiwatar da sakamakon taron ministocin FOCAC na 8 da kuma inganta haɗin gwiwar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, an zartas da haɗaɗɗiyar sanarwa a gun taron, wanda ya ƙunshi ra’ayi ɗaya da Sin da Afirka suka cimma kan martaba ƙa’idojin kundin tsarin MƊD, da nuna adawa da tsoma baki daga waje da saka takunkumi daga ɓangare ɗaya da kuma nuna wariyar launin fata, da kuma kiyaye yin haɗin gwiwa wajen yaƙi da cutar COVID-19 da dai sauransu, wannan ya shaida cewa, ɓangarorin biyu wato Sin da Afirka, suna nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafarsu, ya kuma nuna aniyar Sin da Afirka ta haɗa hannu don gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma a sabon zamani.

Ɓangaren Afirka ya sake nanata bin manufar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da goyon bayan babbar manufar ƙasar Sin ta ɗinkuwar ƙasa, da goyon bayan ƙoƙarin ƙasar Sin na kiyaye ‘yancin kan ƙasa da cikakkun yankunanta, matakin da ƙasar Sin ta yaba sosai.

Fassarawar Zainab