Ana baje kolin mutum-mutumin inji na ƙasa da ƙasa a Beijing

Daga CMG HAUSA

An ƙaddamar da bikin baje-kolin ire-iren mutum-mutumin inji na ƙasa da ƙasa na shekara ta 2022 a jiya Alhamis a nan birnin Beijing, wanda ya samu halartar kamfanonin samar da mutum-mutumin inji, gami da cibiyoyin nazari sama da 130.

Ana baje-kolin wasu mutum-mutumin inji sama da 500 a bikin bana, kana za a ɓullo da wasu sabbin nau’o’in mutum-mutumin inji fiye da 30 a wajen bikin, al’amarin da zai shaida nasarorin ƙirƙire-ƙirƙire, da fasahohin zamani a fannin mutum-mutumin inji.

“Cibiyoyin da suke nuna goyon-baya ga taron mutum-mutumin inji a bana sun dara na shekarun baya,” in ji maitaimakin babban mai bada umurni ga babban taron, wanda kuma shi ne mataimakin sakatare-janar na ƙungiyar nazarin kayan laturonin ƙasar Sin, Liang Liang.
Ya ce, babban taron mutum-mutumin inji na ƙasa da ƙasa, na ƙara taka rawa a duk faɗin duniya, duba da yadda mutum-mutumin inji ke ƙara samun karɓuwa a wasu sana’o’i da dama.

An kuma gudanar da babbar gasar fidda gwani a fannin mutum-mutumin inji ta duniya ta bana, wadda ta ƙunshi wasu fannoni huɗu, ciki har da gasar amfani da mutum-mutumin inji, da gasar tsara fasalin mutum-mutumin inji ta matasa da sauransu.

Fassarawar Murtala Zhang