Haɗin gwiwar Afirka da Sin na taimakawa raya duniya

Daga BELLO WANG

Duniyarmu na fuskantar matsalolin da suka haɗa da yaƙe-yaƙe, da rashin tsaro, da koma bayan tattalin arziki, da ƙarancin abinci, da annoba. Wannan yanayi ya sa ake buƙatar wani mataki da zai taimaka wajen sauƙaƙa yanayin da ake ciki da raya duniyarmu.
To ko haɗin gwiwar ƙasashen Afirka da ƙasar Sin, zai iya biyan bukatunmu a wannan fanni?

An gudanar da taron ƙolin masu tsara aiwatar da ayyukan da suka biyo bayan taron ministoci na 8, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)  ta kafar bidiyo jiya, inda manyan jami’an ɓangarorin Afirka da Sin, suka gabatar da haɗaɗɗiyar sanarwa da jawabai, waɗanda suka nuna yadda haɗin gwiwar ɓangarorin biyu ke taimaka wa raya duniyarmu, musamman ta fannoni 2 dake ƙasa:

Da farko, haɗin kan Afirka da Sin, ya sa ana samun haƙiƙanin ci gaba.
An gudanar da taron ministoci na 8 na dandalin FOCAC a ƙasar Senegal, fiye da watanni 8 da suka wuce.

Sai dai yaya ake aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma wajen taron?

A taro na wannan karo, an yi bayani kan wasu nasarorin da aka samu:

Cikin fiye da watanni 8 da suka wuce, kamfanonin ƙasar Sin sun kammala ayyukan gina wasu manyan kayayyakin more rayuwa a ƙasashen Afirka, da suka haɗa da babbar gadar Fanggioni ta ƙasar Senegal, da tagwayen hanyoyi dake dab da filin jiragen sama na ƙasar Kenya, da babbar hanyar mota ta Kribi-Lolabe dake ƙasar Kamaru, da dai sauransu.

Kana cikin watanni 7 da suka wuce, ƙasar Sin ta shigo da kayayyaki masu darajar dala biliyan 70.6 daga ƙasashen Afirka, da zuba dala biliyan 2.17 ga kasuwannin Afirka.

Ban da wannan kuma, an tanadi ayyukan da za a gudanar da su kamar haka: ƙasar Sin za ta yafe wa wasu ƙasashe 17 dake nahiyar Afirka bashin da take binsu, da samar da ƙarin tallafin abinci ga wasu ƙasashen da suke da buƙata, da ƙara jiragen sama masu ɗaukar fasinjoji, da suke zirga-zirga tsakanin Afirka da Sin, da dai sauransu.

Duk wata yarjejeniyar da aka ƙulla a baya, za a aiwatar da ita. Sa’an nan a yi cikakken bayani kan shirin da za a gudanar, don tabbatar da cika alƙawuran.

Wannan ya nuna yadda ake haɗin gwiwa tsakanin Afirka da Sin don neman hakikanin ci gaba.

Sa’an nan, fanni na biyu shi ne, haɗin gwiwar Afirka da Sin, a buɗe yake ga sauran ɓangarorin.

Shin ko ƙasar Sin tana yin haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka don neman shawo kansu, da samun moriyar siyasa?

Batun ba haka yake ba. Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya bayyana a wajen taron jiya cewa, “Ƙasar Sin na son ganin gamayyar ƙasa da ƙasa sun ci gaba da mai da hankali kan ƙasashen Afirka, da nuna musu goyon baya.

“Idan ƙasashen Afirka sun yarda, za a iya yin haɗin kai tsakanin ɓangarori 3 ko fiye, a nahiyar Afirka.

“Ƙasashen Afirka suna buƙatar wani yanayi na kwanciyar hankali da sada zumunta, maimakon ra’ayin yakin cacar baka, kana suna maraba da haɗin gwiwar da zai amfani jama’a, maimakon shiga takarar wasu manyan kasashe.”

Wannan magana ta nuna yadda ɓangaren Sin ke fahimtar ra’ayin kasashen Afirka.

Ta hanyar yin bincike kan tarihin haɗin gwiwar Sin da Afirka, za mu iya fahimtar cewa, ƙasashen Afirka da ƙasar Sin, sun yi watsi da tunani na yakin cacar baka, wanda har yanzu ƙasashen yamma suke tsayawa a kai.

Sa’an nan sun juya ga tunanin al’ummar dan Adam mai makomar bai ɗaya.

Wanne ne daga cikin su zai fi amfanar al’ummun duniya? Na san kowa zai iya ba da amsa.

Magance saɓanin ra’ayi, da neman cimma matsaya, da ƙoƙarin haɗin gwiwa don daidaita matsalolin da ake fuskanta, da neman samun haƙiƙanin ci gaba, wannan shi ne ra’ayin da zai iya taimakawa, wajen kyautata yanayin da duniyarmu ke ciki, kuma babbar manufa ce da ƙasashen Afirka da ƙasar Sin ke tsayawa a kai, yayin da suke haɗin gwiwa da juna.

Fassarawar Bello Wang