Daniel Amokachi ya halarci babban taron kamfanin Blueprint

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman Kan Harkokin Ƙwallon Ƙafa, Daniel Amokachi ya bi sahun sauran manyan baƙi a taron lacca na shekara-shekara na 2021 na kamfanin Blueprint da aka gudanar a ɗakin taro na International Conference Centre da ke Abuja.

Amokachi ya bi sahun tawagar ministan matasa da wasanni, Sunday Dare domin gudanar da bikin.

An haifi Daniel Owefin Amokachi ne a ranar 30 ga watan Disamba a shekarar 1972 a garin Kaduna da ke arewacin Nijeriya.

Daniel Amokachi ya ci gasar cin kofin nahiyar Afirka sau ɗaya matsayinsa na ɗan wasa, kuma sau ɗaya a matsayinsa na mataimakin kocin Nijeriya.

Da alama ‘ya’yansa biyu waɗanda tagwaye ne sun bi sahunsa domin su ma yanzu suna taka leda yadda ya kamata.

Tarihin Daniel Amokachi da kuma inda ya fito:

Daniel Amokachi, ɗan asalin jihar Kaduna ne wadda ta ke yankin arewacin Nijeriya.

Lokacin da ya ke wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ranchers Bees ta Kaduna ne ya ja hankalin kocin Super Eagles na lokacin, Clemens Westerhof.

A shekarar 1989, Amokachi ya taimaka wa ƙungiyar Ranchers Bees ta lashe kofin gasar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Afirka ta yamma.

Daga nan ne Clemens Westerhof ya saka Amokachi cikin ‘yan wasan da suka wakilci Nijeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka gudanar a birnin Aljiyas na ƙasar Aljeriya a shekarar 1990.

Nijeriya ta samu ta kai wa ga wasan ƙarshe a gasar, amman ta sha kaye a hannun masu masaukin baki, Aljeriya, da ci ɗaya da nema duk da cewa an saka Amokachi a wasan.
Daga nan ne tauraruwar ɗan wasan ta ƙara haskakawa.

Duk da cewa ɗan ƙwallon yana da shekara 16 ne a wancan lokacin, amma ‘yan kallo sun ji daɗin irin zafin naman da ya ke nunawa a hare-haren da ya yi ta kai wa a wasannin da ya buga.

Bayan ficen da ya yi a tawagar Super Eagles a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 1990.

Amokachi bai yi ƙasa a gwiwa ba a gasar da aka yi bayan shekara huɗu, Tunisia 1994, da kuma gasar cin kofin duniya da aka yi a Amurka a shekarar 1994, inda ya yi nasarar zura ƙwallaye biyu a raga.

Amman da aka je gasar cin kofin duniya da aka yi a Faransa a shekarar 1998, sai Amokachi ya samu matsala.

Maikamakon yadda ya taka rawar gani a gasar 1994, gudumawar da ya bayar mai ƙarfi ita ce ƙwallon da ya bai wa Victor Ikpeba ya ci Bulgaria a ɗaya daga cikin wasannin zagayen farko na gasar.

A wani lokacin da ake atisaye kafin wasan ƙarshe a zagaye na farko inda Nijeriya za ta kara da Paraguy, sai gwiwar Amokachi ta goce, kuma aka cire shi daga cikin ‘yan wasan da za su wakilciu Nijeriya a wasa na gaba.

Yadda ya zama koci:

Daga nan Amokachi bai sake taka wani rawan azo a gani a ƙwallon ƙafa ba a matsayinshi na ɗan wasa.

Ya yi aiki a matsayin kocin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na gasar Firimiyar Nijeriya irin su Nasarawa United da Enyimba.

Ya yi aiki a matsayin mataimakin kocin Super Eagles a ƙarƙashin Berti Vogts, amma ya bar muƙamin a shekarar 2008.