Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar jama’atul izalatul bidi’a wa iƙamatul sunnah ta ƙasa reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan yayi wannan kira ne a saƙon sa na taya al’ummar jihar murnan zagayowar babban sallah.
Ya ce ƙungiyar Izala a jihar ta yabawa gwamnati kan yadda ta ɗauki maganar tsaro da muhimmanci.
Sheikh Yakubu Musa ya bayyana kafa jami’an tsaron al’umma (CWC) da gwamnati ta ƙirƙira da samar masu da kayan aiki wanda hakan ya taimaka wajen raguwar ta’addanci a jihar.
Sai yayi kira ga gwamnati da ta ƙara ɗaukan matakan da suka kamata wajen kawo zaman lafiya a jihar.
Shugaban Izalan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bada tasu gudunmawa ga jami’an tsaro da ita kanta gwamnati wajen an yi maganin ta’addanci a jihar da zai kawo dawamammen zaman lafiya.
Ya jawo hankalin malamai musamman na ƙungiyar game da ɓullar wata mummunar aƙida na yan Kur’ani zalla da aka samu bayyanar su da ke da aƙidar ɓatanci ga hadissan Manzo (S.A.W).
Sheikh Yakubu Musa ya ce lalle malamai su ƙara ƙoƙari kan yaƙar wannan mummunan aƙida domin kuɓutar da al’ummar Musulmi daga dukkanin wani sharri da ke cikin ta.
Sheikh Yakubu Musa wanda yanzu haka yana ƙasar Saudiyya inda yake gudanar da aikin Hajji, ya kuma yi kira ga yan siyasa musamman zaɓaɓɓu da su ji tsoron Allah wajen tabbatar da sauke nauyin da Allah ya ɗora masu na al’ummar da suke mulka wajen kawo masu ababen more rayuwa.
Haka iyaye suma su sauke nauyin da Allah ya basu ta yaran su musamman wajen kula da abinda ya shafi tarbiyyar su .
