Jakadan ƙasar Sin: Sin na ingiza tattaunawa kan batun kwance ɗamarar soji

Daga CRI HAUSA

Shugaban karɓa-karɓa na farko na shekarar 2022 na taron tattauna batun kwance ɗamarar soji na birnin Geneva, kuma jakadan ƙasar Sin kan wannan batu, Li Song ya kira cikakken taro yayin da ya yi nasarar kammala wa’adin shugabaci na ƙasar Sin a jiya Juma’a.

Bayan taron, Li Song, ya tattauna da kafofin watsa labarai na birnin Geneva, inda ya bayyana cewa, taron ya kasance dandali ɗaya tilo dake tattauna batun kwance damara tsakanin bangarori daban-daban, inda ƙasashe mambobi 65 ke karɓar shugabanci ɗaya bayan ɗaya. Ya ce ƙasar Sin ta sake zama shugaba ne bayan shekaru 11 da suka gabata, kuma a cikin wadannan shekaru 11, hulɗar ƙasa da ƙasa da yanayin tsaronsu sun fuskanci manyan sauye-sauye, haka kuma kasashen duniya sun fuskanci ƙalubalen da suka hada da tsoffi da sabbabi.

Ya ce a karkashin irin wannan hali, ƙasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ingiza zaman lafiya a fadin duniya, kana tasirinta a ɓangaren kwance damarar soji ya ƙara ƙarfafuwa, a don haka ƙasashen duniya suke sa ran cewa, za ta ci gaba da ba da gudummuwa ga kwance damarar soji tsakanin bangarori daban-daban.

Li Sing ya jaddada cewa, nan gaba ƙasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar samun ci gaba cikin lumana.

Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa