
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba, 12 ga watan Maris ne Hukumar Haɗaka ta bada guraben Karatu ga ɗalibai (JAMB), ta ce za ta fara sayar da takardar neman gurbin karatu na DE (‘Direct Entry’) a jami’o’i, na shekarar 2025.
Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce samun gurbin karatu ta DE abu ne mai muhimmanci ga ɗaliban da suka yi difuloma ko kuma degree kuma suke neman ƙara karatu a fannoni daban-daban a jami’o’in da suke so.
Hakan ya biyo bayan kammala sayar da fom ɗin jarrabawar UTME ne a ranar Asabar, 8 ga watan Maris.
Ya ce, lallai sai ɗalibai sun kiyaye sharuɗɗan da aka gindaya musamman wajen bada bayanansu don kada a samu tsaikon da zai sa ɗalibi ya rasa damar samun gurbi.
Haka kuma, JAMB ta ce za ta naɗa kwamitin da zai tantance takardun da za a gabatar, ta na mai cewa duk wani sakamako na bogi zai sa a ƙi amsa buƙatar bada gurbin ga ɗalibin da abin ya shafa.
Har’ilayau, ta yi kira ga jami’o’i da su tabbatar da tantance dukkanin takardun shaida da ɗalibai za su gabatar a yayin bada adimishon, ya na mai cewa za yi rajista ne kaɗai ta Cibiyar Ƙwararru ta JAMB, wato PRC.
