Mun koya wa yara ‘yan makaranta sana’ar hannu- Hajiya Nafisa Halliru

Spread the love

“Iyaye sun yi farin ciki da muka koyar da ‘ya’yansu sana’a a lokacin karatu”

Daga UMAR AKILU MAJERE 

A makon da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa da jajirtacciyar mace da ya cancanta a kira da Gimbiya, sakamakon irin gwagwarmayar da take yi wurin ganin ta inganta harkar ilimi musamman ma a karkara, duk da cewa ba mazauniyar karkara ba ce, amma tana tafiyayya har zuwa ƙauyukan nesa, waɗanda da yawa ba su da hanyar da mota za ta iya bi.

A cikin tattaunawar, mai karatu da ke bibiyar mu ya ji irin ƙalubalen da Hajiya Nafisa ta fuskanta ciki har da hatsari kan mashin a lokacin da take ƙoƙarin shiga wani ƙauye, da ire-iren waɗannan matsaloli da ya kamata su sare mata gwiwa, saidai ko kaɗan ba ta bari suka yi tasiri ba.

A wannan mako za mu ɗora ne daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: A wancan lokacin kamar ƙauyuka nawa ne kukabyi aiki?

HAJIYA NAFISA: Garuruwan da muka yi gangami da faɗakarwa a wancan lokachin sun haɗa da Unguwar Garko a Hadejia, Auyokayi a Auyo, Garin malan a Maigatari, Dumadumin Toka a Kafin Hausa, Jabarna a Jahun, Kanjua B a Gumel, kafin baka normadic primary school kiyawa, Matara Uku community a Birniwa, Roni, da Gagarawa.

Sauran su ne akwai Islamic Junior Secondary Gwaram mu muka sa wani bawan Allah ya gina ta da ‘toilets’. Gwamnati ta gina ‘toilet’ a JSS ɗan Bulama bayan mun yi ‘town hall meeting’ a Gagarawa LGA.

Bayan wani lokaci sai na buɗe tawa ƙungiyayar mai suna Adolescent Education and Empowerment Initiatiɓe AEEI, na samo mutane jajirtattu muka fara da ‘guidance and counciling serɓice’ a, makarantu, a wannan lokachin mun yi a makarantar gadadin da ‘senior secondary school’ Baure a nan Dutse LGA, muka fara buga littafai muna raba wa makarantar ‘primary’, na manta wasu makarantun, amma na tuna da makarantar Dakta Nuhu Muhd Sunusi ‘primary school’ da ke wa laƙabi da makarantar Danbe kan titin shagunan baba chaichai da ke Dutse.  

Sai kuma na nemi tallafi daga Donor Agencies kamar Palladium, a inda na sami talafin miliyan biyar don gudanar da wani ‘program’ da na sa wa suna ‘in school skills acƙuisition for Adolescent girls’. Muka siyi kekunan ɗinki da na saƙa, da zare da allura, da kuma duk abinda mutun yake buƙata, don koyan ɗinki da saƙa, muka zaɓi makarantu biyu a miga, wato Dangyatin da Hantsu da Ringim, muka zaɓi karwai da katutu, sai kuma malan Madori senior da junior secondary school inda yara cari suka amfana a kowane makaranta da wannan horo ya shafa a duk makarantun.

Wannan aikin ya yi kyau sosai gaskiya, iyaye sun yi farin ciki da wannan program ɗin, saboda ‘ya’yansu sun koyi aikin hannu a lokaci guda da suke karatu. Kuma project ɗin wata tara aka yi aka gama.

Menene matsayin shirin AEEI da ku ka yi aiki da shi? 

AEEI kamar ‘ya take a wuri na, duk sanda na sami dama inna bada gudunmawa gwargwadon abinda zan iya ta wannan ƙungiya.

AEEI ni member ce a JISCAP, wato haɗakar ƙungiyoyin da suke ‘adɓocacy’ a Jigawa state, kuma member ce ta JISOP, wato haɗakar ƙungiyoyin da ke kula da haƙƙin mutane masu buƙata ta musamman. 

AEEI member ce ta NetJiC, wato haɗakar ƙungiyoyin da ke aiki a kowane fanni na rayuwa, kamar ilimin, lafiya, ‘gender’ da sauran su.

AEEI member ce ta NACTAL wato, haɗaɗɗiyar ƙungiyar nan ta ƙasa mai yaƙi da cin zarafin ‘ya’ya mata da ƙananan yara. 

AEEI member ce a haɗaɗɗiyar ƙungiyar nan ta AONN da ke fafutuka da ta kula da marayu yan ƙasa.

Kuma alhamdulilla Allah ya ba ni dama na zama;

1. Ni ce gender officer ta NetJiC.

2. Na zama member ta white paper committee da gwamna ya naɗa don duba halin da manyan makarantun Jihar Jigawa ke ciki da kuma ba da shawara kan abinda ya kamata gwamnati ta yi, mun yi mungama lafiya, alhamdulillah.

3. Nazama member ta committee da muka bincike ayyukan J CARES don ba wa gwamnati shawara kan matakin da za ta ɗauka akan masu laifi a wannan harkar, kuma mun yi iyakacin bakin ƙoƙarin mu. alhamdulillah.

4. Ni member ce ta OGP, wato Open Goɓernment Partnership a Jigawa.

Haka zalika ni ce Coordinator ta AONN a Jihar Jigawa, wato Association of Orphan and ɓulnerable Children in Nigeria.

In an tashi neman ki ta yaya za a iya samun ki?

Za a iya samuna ta waya ko ta hannun wakilin wannan jaridar a shirye nake na bada dukkan gudunmawar da ake da buƙata

To mungode.

Ni ma na gode.

By ukarofi